Mai Siyar da Man Fetur Ya Cinna Wa Abokinsa Wuta a Kan Cajar Waya
- Wani mutum ya yi aikin dana-sani yayin da ya bankawa abokinsa wuta bayan da suka samu wata 'yar husuma
- An ruwaito cewa, wannan lamarin ya faru ne a jihar Akwa Ibom, kuma 'yan sanda sun tabbatar da faruwarsa
- Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da bincike kan lamarin da kuma yadda za a gurfanar da mutumin a gaban kuliya
Jihar Akwa Ibom - Wani mai siyar da man fetur a bakin hanya mai suna Akpan Okon Akpan ya kone abokinsa kurmus har lahira bayan samun sabani da suka yi.
An ruwaito cewa, Akpan ya kashe abokin nasa ne akan cajar waya, kamar yadda jarida Punch ta ruwaito.
A cewar rahoto, Akpan ya bankawa Junior Ime Philip wuta ne kana ya bar shi har ya mutu, kamar yadda ‘yan sanda da shaidu suka fada.
Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta tabbatar da faruwar lamarin bayan da jami’anta suka tabbatar da damke mutumin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da ake gabatar da mai laifin a gaban manema labarai a hedkwatar ‘yan sanda da ke Uyo, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olatoye Durosinmi ya ce wanda ake zargin antayawa abokin nasa fetur ne kana ya cimma masa shana.
'Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin
A cewar kwamishinan, wannan lamarin ya faru ne a yankin Ikot Ekwere Ubium a karamar hukumar Nsit Ublum na jihar da misalin karfe 6:30 na yamma a ranar 15 ga watan Disamban 2022, Daily Post ta tattaro.
Da yake bayanin abin da ya faru, wanda ake zargin ya ce:
“Ban san mutumin ba a baya, ya shigo shago na sannan yace yana neman wani ne zai karbi caja, na fada masa mutumin ba ya cikin shago na. Cikin fushi, ya dauki kwalba ya tunkare ni da fada, nima na biye masa.
“Na yi amfani da fetur din da nike siyarwa na jika shi dashi, gaskiya bansan abin da nake aikatawa ba har sai da ya fara konewa kuma gashi mutane sun taru, muna ta kokari kashe wutar amma lokaci ya kure saboda sadda suka kai shi abisiti, ya mutu a can.”
Ana yawan samun tashin wuta, gobara ko tashin hankalin da ke da alaka da wuta a Najeriya, a jiya ne gobara ta kame wani asibiti.
Asali: Legit.ng