Yan Bindiga Sun Tashi Bama-Bamai a Hedkwatar 'Yan Sanda a Imo
- Yan bindiga sun kai hari tare da ta da bama-bamai a hedkwatar yan sanda ta Atta, karamar hukumar Njaba, jihar Imo
- Wannan harin ya zo ne awanni bayan an kaiwa tsohon gwamnan jihar Mummunan hari, aka kashe yan sanda 4
- An ce maharan sun taba kona Ofishin 'yan sandan a watan Yuni, 2021 bayan sun kone Kotu guda biyu dake wurin
Imo - Miyagun 'yan bindiga sun kone babban Ofishin 'yan sanda na yankin Atta a karamar hukumar Njaba da ke jihar Imo, kudu maso gabashin Najeriya ranar Litinin da daddare.
Wannan na zuwa ne awanni bayan mummunan harin da aka kaiwa ayarin tsohon gwamnan jihar, Ikedi Ohakim, inda yan sanda hudu dake tare da shi suka mutu.
Sai dai a wannan sabon harin, wata majiya daga yankin da abun ya faru ta shaida wa wakilin jaridar Punch cewa 'yan bindiga sun kutsa hedkwatar 'yan sandan suka rika jifa abubuwan fashewa suna tashinsu.
Rahotanni sun bayyana cewa ba bu jami'an dan sandan da ke aiki a lokacin da 'yan ta'addan suka aikata wannan mummunar ta'asa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Majiyar ta kara da cewa:
"Hedkwatar 'yan sanda ta garin mu ta kone kurmus, jiya da daddare aka kona ta, ba bu wanda ya iya fitowa ya kawo dauki saboda fargaba, a yanzu da nake zancen mutane sun tarwatse a yankin"
Legit.ng Hausa ta gano cewa a watan Yuni na shekarar 2021, yan ta'adda sun yi kaca-kaca da wannan Ofishin 'yan sandan bayan sun kone Kotu guda biyu da ke gefenta.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Imo, Micheal Abattam, bai ce komai ba game da harin a hukumance har zuwa yanzu da muka hada muku rahoto.
Tsohon gwamna Imo ya sha da kyar
A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Farmaki Ayarin Tsohon Gwamnan Imo, Sun Kashe 'Yan Sanda
Tsagerun 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun kai wani mummunan farmaki kan ayarin tsohon gwamnan jihar Imo, Ikedi Ohakim, ranar Litinin din nan da ta gabata.
Bayanai sun ce tsohon gwamna, wanda ya kubuta daga sharrin maharan, an ce bam maharan suka dasa a Motar dake mara masa baya haka ya yi ajalin dakarun 'yan sanda hudu.
Asali: Legit.ng