Yar Baiwa: Hotunan Kyakkyawar Yarinyar Da Aka Haifa Da Idanu Masu Launin Shudi Ya Yadu

Yar Baiwa: Hotunan Kyakkyawar Yarinyar Da Aka Haifa Da Idanu Masu Launin Shudi Ya Yadu

  • Wata yar Najeriya da aka haifa da idanu na musamman ta yi fice a intanet kuma mutane sun mato a kanta
  • An haifi yarinyar mai shekaru 7 da idanu mai launin shudi da kyalli kuma ita kadai ke da irin shi a gidansu gaba daya
  • Hotunanta sun sburge masu amfani da soshiyal midiya amma wasu na ganin akwai wani al'amari tattare da kamanninta

Wata yarinyar mai shekaru 7 da aka ambata da suna Wasilat ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya saboda yanayin idon da Allah ya halicceta da shi.

Tima Wire ta ci karo da kyakkyawar yarinyar sannan ta wallafa hotunanta a shafin Facebook na Rant HQ Extention bayan ta matukar burge ta.

Yarinya mai dauke da idanu launin shudi da wata matashiya
Yar Baiwa: Hotunan Kyakkyawar Yarinyar Da Aka Haifa Da Idanu Mai Launin Shudi Ya Yadu Hoto: Tima Wire
Asali: Facebook

"Wow yarinyar da na hadu da ita a yau tana da matukar kyau da kwayan idanunta," Tima ta rubuta yayin da ta wallafa hotunan yarinyar."

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Ginawa Iyayenta Dankareren Gida Na Gani Na Fada, Bidiyon Ya Yadu

A ranar 31 ga watan Disamba, Tima ta sake wata wallafa da yarinyar a shafin inda ta dungi yabon kwayoyin idanun Wasilat.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tima ta bayyana cewa sabanin abun da mutane da dama ke hasashe cewa yarinyar ta yi amfani da kwayar idon bogi ne, haka Allah ya halicce ta.

Lokacin da Legit.ng ta tuntube ta, Tima ta bayyana cewa ta hadu da Wasilat ne a kauyen mahaifiyarta.

"Sunanta Wasilat koda dai bata da wani alaka da ni kawai dai na hadu da ita ne a kauyen mahaifiyata sai na yanke shawarar daukarta hoto sannan na saki hotunan don ganin ikon Allah."

Tima ta kara da cewar ta tabbatar ance daga Kogi take cewa wannan ba cuta bane, amma cewa an haifeta ne a haka.

"Shekarunta 7 kuma ita kadai ce da irin shi a gidansu. Daga jihar Kogi take kuma da shi aka haife ta."

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Budurwa Ta Shiga Aikin Soja, Hotunan Sauyawarta Sun Yadu

Jama'a sun yi martani

Ben Sigie ya ce:

"Yar baiwa."

Quin Ria ta ce:

"Ita din ta daban ce."

Echero Favour ta ce:

"Idanunta na da kyau amma yana iya shafar jinta a gaba amma muna rokon kada Allah yasa hakan ya faru."

Peace Njoku ta ce:

"Dubi idanun da nake kashewa kudina. Rayuwar nan ba sauki."

Budurwa ta ginawa iyayenta dankareren gida

A wani labarin, wata matashiyar budurwa ta gwangwaje iyayenta da wani hadadden gida na kerewa sa'a.

Kamar yadda budurwar ta bayyana, ta jima tana mafarkin cika wannan buri nata na yiwa mahaifanta abu na musamman.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng