'Yan Sanda Sun Kashe ’Shugaban ’Yan Bindiga a Katsina, Sun Kwato Alburusai da Kudade
- Kasurgumin shugaban 'yan bindiga ya rasa ransa yayin da ya jagoranci wani hari a kan wasu jami'an 'yan sanda a Katsina
- An jikkata wasu 'yan sanda, an kuma kwato makamai da kudade a hannun 'yan bindigan da suka kawo harin
- Jami'an tsaro a Najeriya na ci gaba da samun nasara kan 'yan ta'adda a yankuna daban-daban na kasar nan
Jibia, jihar Katsina - Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta kashe dan kasurgumin dan bindiga bayan kai wani babban hari kan jami’an tsaro a jihar, TheCable ta ruwaito.
Gambo Isah, kakakin rundunar ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin 02 ga watan Janairun 2023.
A cewar Isah, ‘yan bindigan sun farmaki wasu jami’an ‘yan sanda a kusa da hanyar Jibia a karamar hukumar Jibia ta jihar da misalin karfe 4:30am a ranar Litinin.
Ya kuma bayyana cewa, jami’an ‘yan sandan sun dakile harin, tare da kashe babban shugaban ‘yan bindigan duk da an jikkata wasu jami’an ‘yan sanda biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar 'yan sanda ta bayyana abin da ya faru
A cewar sanarwar:
“Da misali karfe 4:30am, ‘yan ta’adda masu yawa, sun yi harbin kan mai uwa da wabi, sun farmaki matsayar ‘yan sanda a mahadar Magama-Hirji, kusa da hanyar Jibia.
“’Yan sanda sun yi kazamar bata-kashi da ‘yan ta’addan kuma sun yi nasarar dakile su.”
“An hallaka daya daga cikin ‘yan ta’addan, kuma an kwato AK-47 da jakar makamai masu alburusai 90 masu girman 7.62mm na AK-47.
“An kwato kudade da wasu kayayyakin aikata laifi. Da yawan ‘yan ta’addan sun tsere da raunukan harbin bindiga.”
“’Yan sanda biyu sun samu raunuka yayin wannan arangama. An dauke su zuwa asibitin Jibia, an lura da raunukan, an kuma sallame su.
“Tawagar bincike na ci gaba da kakkabe yankin domin kamu ko tattaro gawarwakin ‘yan ta’addan. Ana ci gaba da bincike.”
A wani rahoton Channels Tv, kakakin ya ce dan bindigan da aka sheke shine ake zargi da kitsa harin watan Fabrairun bara da ya kai ga mutuwar Abdulkadir Rano, jami’in yanki na ofishin ‘yan sandan Jibia.
Har ila yau, 'yan bindiga sun sace wani jigon siyasa a jihar Zamfara, kuma sun yi awon gaba da 'ya'yansa biyu tare dashi.
Asali: Legit.ng