Wasu ’Yan Bindiga Sun Sace Kanar Din Soja Mai Ritaya da Yaransa Biyu a Jihar Zamfara
- Wasu kasruguman 'yan bindiga sun yi awon gaba da wani jigon siyasar jihar Zamfara a Arewa maso Yamma
- An sace Kanar Rabiu Yantodo mai ritaya tare da wasu 'ya'yansa biyu a hanyarsa ta zuwa garinsu a jihar Lahadi
- Rahoto ya bayyana cewa, Yantodo ne babban mai hamayya da komawar Sanata Kabiru Marafa kan kujerar sanata a bana
Gusau, jihar Zamfara - Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wani tsohon Kanar din soja, Rabiu Yandoto tare da wasu ‘ya’yansa biyu a hanyar Gusau zuwa Tsafe a jihar Zamfara.
Wani mazaunin yankin, Mohammed Hassan ya bayyana cewa, Yantodo na kan hanyarsa ta zuwa garinsu ne tare da ‘ya’yansa biyu a ranar Lahadi 1 ga watan Janairu da dare lokacin da ‘yan bindigan suka tattara shi zuwa cikin daji.
Majiyar ta bayyana cewa, tun farko ‘yan bindigan nufinsu ba komai bane face yin awon gaba da wannan jigon siyasa na jihar Zamfara, rahoton Punch.
Yadda aka sace Yantodo
A cewar Hassan:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“’Yan bindigan sun yiwa Kanar din mai ritaya kwanton bauna a daren Lahadi kuma suka yi garkuwa dashi da ‘ya’yansa biyu da wasu mutane.
“Mun ji karar harbin bindigogi sai muka fara gudu zuwa daji saboda tsoron ‘yan bindigan amma daga baya muka gano Kanar Yantodo ne suke nema.”
Wanene Kanar Yantodo?
Yantodo dai babban abokin hamayyar Sanata Kabiru Marafa na siyasa kuma yana gangamin adawa da komawar sanatan kan kujerarsa a zaben 2023 mai zuwa.
Shine shugaban tawagar siyasar ‘Wake da Shinkafa’ ta jam’iyyar APC, wacce manufarta itace tabbatar da Kabiru Marafa bai lashe zaben sanata ba a 2023.
An yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, amma ba a yi nasarar hakan ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
'Yan bindiga sun sace basarake da limami a hanyar zuwa taron APC
A jihar Katsina kuwa, 'yan bindiga sun sace wani barasake tare da wasu mutane biyu da suke tare dashi a hanyar zuwa taron APC.
Rahoton da muka samo, an ce 'yan bindigan sun kira ahalin basaraken tare da bayyana musu cewa yana hannu.
Jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya na yawan fama da hare-haren 'yan bindiga a cikin 'yan shekarun nan.
Asali: Legit.ng