Nagode Ina Raye: Bidiyon Mai Kafa Daya da Yake Tuka Keke Ya Birge Jama'a
- Wani mutum ya kara godewa Ubangiji da ya bar masa rai da lafiyarsa bayan ya ga wani mutumi na tuka keke da kafa daya
- Wani faifan bidiyon da Kaplorg PC ya wallafa ranar Laraba 28 ga watan Disamba, an ga matukin keken na sarrafata cikin siga ta kwarewa kan babban titi
- Mutumin ya ce ya hango gurgun ne yayin da yake kan hanyarsa ta komawa gida, inda ya yanke shawarar daukarsa bidiyo wanda a yanzu sama da mutane 41,600 suka duba
Masu amfani da kafar sada zumuntar TikTok suna ta martani game da bidiyon wani mai kafa daya kan keke yana tuka ta cike da kwarewarsa.
Matukin keken wanda gurgu ne mai kafa daya na tukin ne cikin siga ta kwarewa a babban titi kamar kafafu biyu cikakku gare shi.
Kanwar Maza: Yadda Matashi Ya Kwanta a Bakin Gate Tare Da Garkame Shi Don Hana Maneman Auren Kanwarsa Shiga
Sai dai kawai idan aka matso kusa ne za a gane karara matukin keken ya rasa kafa daya.
Kaplorg PC, mai amfani da kafar sada zumuntar wanda ya wallafa faifan bidiyon ya ce ya kara godiya ga Ubangiji da ya bashi tsawon rayuwa da lafiya duba da yadda ya ga matukin keken cikin farin ciki yake tukawa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
'Yan dandalin TikTok da dama da suka kalli yadda mutumin ke kokarin tuka keken sun ce bidiyon ya taba zukatansu.
Jama'a sun yi martani
Daga ranar Alhamis, 29 ga watan Disamba, bidiyon ya samu jinjina 2,400 da wadanda suka kalla 41,600 a TikTok ne
Martanin jama'a:
@golddestiny8 ta ce:
"Ubangiji da girma yake."
@hannabenz34 tayi tsokaci:
"Nagodewa Jesus da ya barni da rai na."
@bigta55 ta ce:
"Taya haka ya yuwu."
@Pablo Richie yayi tsokaci:
"Nagode maka Ubangiji da ka bani kyautar rayuwa."
Yana aji 3 ya Gane Babu Sunansa a Rijista
A wani labari na daban, wani dalibin jami'ar Nsukka ya bayyana yadda yana aji uku a jami'ar ya fahimci cewa babu sunansa a rijistar jami'ar baki daya.
A cewar matashin, ya je canza kwas din da yake yi ne shiyasa ya gane cewa babu sunansa a rijistar jami'ar baki daya.
Jama'a sun dinga mamakin labarin matashin duk da wasu sun ce hakan ba bakon abu bane.
Asali: Legit.ng