Ku Tashi Tsaye, Ku Nemi Makami Ku Kare Kanku, Shahararren Gwamnan Arewa Ya Fada Wa Mutanen Jiharsa
- Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya shawarci mutanen jiharsa su tashi su kare kansu daga yan bindiga da ke kawo musu hare-hare
- Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ziyarci fadar Hakimin Duguri, a karamar hukumar Alkaleri
- Mohammed ya ce nan ba da dadewa ba gwamnatinsa za ta tallafawa mutanen da ababen zirga-zirga da makamai don su kare kansu
Bauchi - Kawo yanzu, yan bindiga sun kashe a kalla mutane 20 a harin ramuwar gayya, sun kuma raunata wasu a kauyuka da ke Duguri a karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi, Daily Trust ta rahoto.
A baya-bayan nan, yan sandan jihar Bauchi tare da yan banga sun shiga daji sun kashe yan bindiga 12 ciki har da shugabansu, wanda ya dade yana adabarsu.
Dattijon Arewa Mai Karfin Fada A Ji Ya Bukaci Yan Najeriya Su Yi Watsi Da Kiran Sarkin Daura Kan Zaben 2023
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, wanda ya ziyarci wurin a ranar Alhamis, ya bayyana lamarin a matsayin abin da ba za a amince da shi ba kuma abin bakin ciki, Nigerian Tribune ta rahoto.
A jawabinsa a fadar Hakimin Duguri, Alhaji Adamu Mohammed Duguri, gwamnan ya koka kan yadda yan bindigan ke hana yin noma.
Bala Mohammed ya bukaci mazauna yankin daga yanzu 'su tashi tsaye, su nemi makamai kuma su kare kansu'.
"An san ku a matsayin mazaje; kada ku bari wadannan bata garin su ci galaba kanku. Ku kare kasarku kuma ku yantar da kanku."
Ya kuma bukaci mutanen su bincika kansu su zakulo bata gari da ke aiki a matsayin yan leken asiri ga yan bindigan, yana mai cewa ba za su iya kawo hari ba sai da yan leken asiri.
Gwamnan ya bada tabbacin gwamnatinsa za ta cigaba da aiki tare da jami'an tsaro a jihar don kare lafiya da dukiyoyin mutanen jihar.
Gwamna Bala ya jinjinawa mutanen Kafin Duguri saboda kare kansu
A Kafin Duguri, gwamnan ya jinjinawa mutane saboda tashi tsaye su kare kansu daga yan bindigan da suka kawo musu hari.
Ya ce:
"Na san ku jarumai ne har da matanku. Ku tashi tsaye, ku kare kanku har da makwabtanku daga yan bindiga.
"Haka ya kamata. Mu kare kanmu daga yan bindiga da bata-gari. Abin da kuka yi dai-dai ne kuma ku cigaba da yin hakan da makwabtanku.
"Daga yanzu duk wanda ya taho wurin ku zai kawo muku hari ko zai kashe ku, ku kare kanku."
Gwamnan kuma ya ce nan bada dadewa ba gwamnatinsa za ta taimakawa mutane da ababen zirga-zirga da makamai don su kare kansu daga mahara.
Jami'an tsaro sun dakile harin yan bindiga a Zamfara
A wani rahoton, yan sanda a Zamfara sun yi nasarar dakile harin da yan fashin daji suka kawo har sau biyu a kananan hukumomin Shinkafi da Zurmi.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sanda, Muhammad Shehu ya sanar da hakan yayin holen masu laifi a ranar Asabar a Gusau, rahoton Channels TV.
Asali: Legit.ng