A Farmakin Kwana 3 a Jere, 'Yan Bindiga Sun Halaka Jama'a Sun Sace 50 a Sokoto

A Farmakin Kwana 3 a Jere, 'Yan Bindiga Sun Halaka Jama'a Sun Sace 50 a Sokoto

  • 'Yan bindiga suna cigaba da cin karensu ba babbaka a kauyukan kananan hukumomin Goronyo, Gada da Sabon Birni dake jihar Sakkwato
  • Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa hare-haren sun gabata tsakanin Litinin zuwa Laraba, yayin da hatsabiban suka auka yankunan gami da budewa jama'a wuta
  • Sun halaka tare sace mutane da dama daga bisani jami'an tsaron suka dakilesu yayin shiga Gatawa duk da suna tilasta jama'a biyan haraji kafin su yi noma

Sokoto - An ruwaito yadda 'yan bindiga suka halaka mazauna yankin Goronyo da kananan hukumomin Gada da Sabon Birni da dama dake jihar Sakkwato.

Yayin zantawa da The Cable, Lukman Iliyasu, wani mazaunin yankin Sabon Birni, ya bayyana yadda hare-haren suka gabata tsakanin Litinin zuwa Laraba.

Taswirar Sokoto
A Farmakin Kwana 3 a Jere, 'Yan Bindiga Sun Halaka Jama'a Sun Sace 50 a Sokoto. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Iliyasu ya ce 'yan bindiga masu tarin yawa sun fada yankunan, inda suka budewa mutane wuta, wanda hakan ya janyo mutane da dama suka samu raunuka daban-daban.

Kara karanta wannan

Wani Gwamnan Ya Sake Rokon 'Yan Bindiga Su Aje Makamai Gwamnatinsa Zata Yafe Masu

"Hare-haren sun auku ne tsakanin Litinin zuwa Laraba. Kauyukan da farmakin ya shafa na karamar hukumar Goronyo, Gada da Sabon Birni."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

- Kamar yadda ya shaidawa The Cable.

"Kauyukan da aka hara a Sabon Birni su ne Dan Gari inda aka halaka mutane bakwai gami da sace mutane da dama, a Kurawa an halaka mutane biyu gami da yin garkuwa da mutane da dama, sannan kauyen Gumozo, an halaka mutane uku tare da sace mutane da dama.
"Suna kokarin aukawa Gatawa yayin da jami'an tsaro suka dakilesu, sannan na gano yadda aka sheke 'yan bindiga da dama yayin musayar wutar.
"Yan bindiga sun halaka mutane da dama gami da yin awon gaba da sama da mutane 50 daga wasu kauyuka. Ka san yadda suke aiwatar da harinsu, sun auka yankuna da dama a kwanaki daban-daban. Sun dauki tsawon lokaci suna kai farmaki Sabon Birni. Har ma haraju suka sanyawa yankunan mu.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Bayyana Abu 1 Da Yan Kaduna Ba Za Su Taba Manta El-Rufai a Kansa Ba

"Wannan ita ce shekara ta biyu da suka wajabta mana haraji. Sun ce ba za su bar manomanmu zuwa gona ba su yi shuka ko girbi ba.
"A shekarar da ta gabata, sun wajabtawa Sabon Birni biyan N3 miliyan saboda tsabar yawanmu, amma N1.5 miliyan kadai muka iya biya. Wannan shekarar, sun bukaci mu biya N2 miliyan saboda rayuwar yawanmu yayin da mutane da dama suka rasa rayukansu da wasu da dama da aka tilasta musu biyan N1 miliyan."

Kabir Dauda, wani 'dan majalisa me wakiltar gabashin Gada a majalisar jihar Sakkwato, a wani zantawa da manema labarai a gidan radiyon FM, ya ce daga cikin mutane 50 din da aka yi garkuwa mata da yara ne kuma har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane.

Dauda ya kara da bayyana yadda 'yan bindigan suka bukaci a biyasu N5 miliyan kafin su saki kowannensu.

'Dan majalisar yayi kira ga hukumomin tsaro da su turo da jami'ansu yankunan, inda ya ce "babu abun da aka yi don kare rayuwar wadannan mutanen."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Halaka Manoma 4, Sun Tasa Keyar Wasu 100 Kan Kin Biyan Kudin Haraji

Duk iya kokarin da aka yi don tuntubar kakakin 'yan sandan jihar Sakkwato, Sanusi Abubakar don jin ta bakinsa bai yi tasiri ba, bai amsa kiraye-kirayen waya ko sakonnin kar ta kwana da aka aika masa dasu ba.

'Dan takarar majalisa ya ziyarci wadanda soja suka yi wa luguden wuta a Zamfara

A wani labari na daban, 'dan takarar majalisar dattawa na yankin Bungudu/Maru a jihar Zamfara ya ziyarci wadanda sojaoji suka yi wa luguden wuta bisa kuskure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng