Launi Kadai Aka Sauya, Inji Wata Matar da Ta Manta da Sabbin Naira a Aljihu Aka Wanke
- Wata fitacciyar ‘yar Twitter, @Fluffy_Naz ta ce akwai yiwuwar gari ko ruwan launi kadai aka zuba kan sabbin Naira da aka buga saboda suna wankewa
- Artist Chinazo ta bayyana yaddda ‘yar uwarta ta mance kudin a cikin tufafi sannan aka wanke, lamarin da ya sauya kamannin kudin
- Hoton yadda kudin ya sauya daga launin zuwa fari tas ya ba jama’a mamaki a Twitter, an caccaki CBN
Wata fitacciyar ‘yar wasan kwaikwato ta bayyanawa ‘yan Najeriya abin da ya faru lokacin da ‘yar uwarta ta manta sabbin Naira a aljihu, aka wanke.
A cewarta, kanwarta ce ta manta da kudin a cikin aljihu, kuma har aka wanke kudin, lamarin da ya sauya launin kudin zuwa farar takarda.
Ta rubuta a shafin Twitter cewa:
“To ga dai ‘yar uwata ta manta sabbin kudi a aljihu sannan aka wanke su, wannan ne yadda kudin ya koma! Idan ruwan sama ya yi maka duka kuma wannan kudin ne kadai fatanka, ka kade kawai.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kalli hoton:
Jama’a sun yi martani a kai
hairess_gallery:
“Akwai tarin kudaden bogi dake yawo a yanzu.”
hayuurr:
“Wannan ai bolar kamfani ne bayan dogon kwalliya da sanya launuka.”
sweetylyx_official:
“Iana fada miki kawai launi suka sauya.”
mufasa__forever:
“Da dutse ta yi amfani wurin wankin ne? Ko kuma CBN sun yi kudin da abubuwan da basu da kargo.
officialmikemore:
“Dama tun farko munsan dauri ne da rini kawai suka yi.”
_cici_nita:
“Ba za su iya amfani da launin asali ba. Wannan wane irin matsala ne???”
db_naturals_:
“Ba su iya yin aiki mai kyau a kansa ba ma. Akalla idan kuna son sauya Naira, sai a yi shi ta hanyar da ta dace mana. Kalli yadda kudin suke fa kamar wasa.”
Ba mu san adadin sabbin Naira da aka buga ba, inji CBN
A wani labarin kuma, mataimakiyar gwamnan CBN ta ce ba a san adadin kudaden da babban bankin Najeriya yta buga ba.
Wannan na zuwa ne a wani ganawa da ta yi da 'yan majalisun kasar nan don ba da bahasi ga halin da ake ciki na kayyade kashe kudi.
'Yan Najeriya na ci gaba da dasa alamar tambaya kan halin da ake ciki a kasar nan bayan sauya Naira.
Asali: Legit.ng