Gwamnan Legas Ya Gana da Sufeta Janar da Yan Sanda Kan Kisan Lauya
- Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya gana da Sufetan yan sanda na kasa, Usman Baba a birnin tarayya Abuja
- Manyan kusoshin guda biyu sun tattauna ne kan batun yadda za'a bullo wa kisan da wani dan sanda ya yi wa Lauya a Legas
- IGP ya mika sakon ta'aziyya ga iyalai da abokan arzikin marigayya, yace za'a dauki mataki kan wanda ya aikata
Abuja - Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Oluz, ranar Alhamis ya gana da Sufetan 'yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba a Louis Edet House da ke Hedkwatar 'yan sanda Abuja.
Jaridar Punch ta rahoto cewa gwamnan ya gana da IGP ne kan kisan da wani ɗan sanda ya yi wa lauya a jihar Legas kana ya nemi a dauki matakin bi mata hakkinta.
A wata sanarwa, kakakin rundunar 'yan sanda ta ƙasa, Olumuyiwa Adejobi, yace mutanen biyu sun tattauna yadda za'a bi wajen hanzarta yi wa mamaciyar adalci.
Adejobi yace yayin da IGP ke miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai, yan uwa da abokan arzikin lauyar, ya tabbatar da cewa hukumar yan sanda ba zata yi kasa a guiwa ba har sai an mata adalci.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sufetan ya kara da jaddada cewa tuni hukumar ta fara aiki kafaɗa da kafaɗa da Antoni Janar na jihar Legas domin gurfanar da duk masu hannu a kisan gaban Kotu, doka ta yi aikinta.
Adejobi ya ce:
"A masa martanin gwamnan Legas ya yi alkawarin taimaka wa hukumar 'yan sanda wajen tabbatar daan yi adalci a Kes din kuma zasu haɗa kai a wayarwa mutane kai kan fahimta da sanin doka don gila alaka mai kyau da jami'an tsaro."
"Ya jaddada cewa gwamnatinsa zata haɗa guiwa da hukumar wurin shirya horo ga jami'an 'yanda, da kwasa-kwasai kan kowane bangare na aikin yan sanda."
Yanzu-Yanzu: Kotun Karar Zabe Ta Fatattaki Segun Oni, Tace Oyebanjin APC ne Ya Lashe Zaben Ekiti na Gwamna
"Daga nan sai IGP ya bukaci jami'an yan sanda da su rika bin doka sau da kafa kuma kula game da hakkin mutane. Ya kuma roki daukacin al'umma su rika ba jami'an tsaro haɗin kai a kokarinsu na kawo karshen aikata muggan laifuka."
PSC ta Dakatar da ‘Dan Sandan da Ake Zargi da Bindige Lauya a Legas
A wani labarin kuma Hukumar jin dadin 'yan sanda ta amince da dakatar da dan sandan da ya harbe wata lauya a jahar Legas
Dakatarwan na zuwa ne bayan sa’o’i kadan da Usman Baba Alkali, Sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya ya bukaci a ɗauki wannan matakin kan mai laifin.
Asali: Legit.ng