Allah Ya Yi Wa Tsohuwar Sarauniya Kyau Ta Najeriya Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Tsohuwar Sarauniya Kyau Ta Najeriya Rasuwa

  • Allah ya yi wa tsohuwar sarauniyar kyau ta Najeriya, Mrs Foluke Abosede Ntukdem, rasuwa
  • Marigayiyar ta rasu cikin barcinta tana da shekaru 75 a duniya kamar yadda dan ta ya tabbatar
  • Mrs Foluke Abosede Ntukdem ce ta lashe gasar sarauniyar kyau ta Najeriya a 1968 kuma ta wakilci Najeriya a gasar kyau da aka yi a kasar Birtaniya

Jihar Legas - Tsohuwar sarauniyar kyau ta Najeriya, Mrs Foluke Abosede Ntukdem, ta rasu cikin kwanciyan hankali a barcinta a gidan da ke Jihar Legas.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa ta rasu a ranar Litinin, 19 ga watan Disamban shekarar 2022, kamar yadda iyalanta suka tabbatar.

Foluke
Tsohuwar Sarauniyar Kyau Ta Najeriya Ta Rasu Tana Da Shekaru 75. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta rasu tana da shekaru 75 a duniya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Matar Fitaccen Jigon APC A Legas Ta Mutu Ba Zato Ba Tsammani

Marigayiyar ta wakilci jihar ta yamma a gasar sarauniyar kyau kuma ta lashe gasar ta zama sarauniyar kyau ta Najeriya a shekarar 1968.

Ta kuma wakilci Najeriya a gasar sarauniyar kyau na duniya karo na 18 da ake yi a babban birnin Birtaniya a Nuwamban shekarar 1968, inda sarauniyar kyau ta Australiya, Penny Plummer ta yi nasara cin gasar.

Dan marigayiyar sarauniyar kyau din ya tabbatar da rasuwarta

Mr Mfon, dan marigayiya Foluke Ntukidem ya tabbatar da rasuwar tsohuwar sarauniyar kyau din yayin da wakilin Premium Times ya tuntube shi, ya ce cikin barcinta ta mutu.

Ga Kalamansa:

"Mahaifiyata, Mrs Foluke Abosede Ntukidem (neeOgundipe) ta rasu a ranar Litinin da ya gabata, 19 ga watan Disamban 2022, tana da shekaru 75.
"Ita ce sarauniyar kyau ta Najeriya a shekarar 1968. Muna kammala shirye-shirye da zaben hotunan ta da za mu raba da zarar mun gama."

Hadimin Gwamna Abdullahi Sule ya riga mu gidan gaskiya

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: NBA Ta Bukaci a Biya Iyalan Lauya Da Aka Kashe Diyyar N5b, Ta Ba Da Kwakkwaran Dalili 1

A wani rahoton, Alhaji Murtala Lamus, mashawarci na musamman kan ayyuka ga Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya riga mu gidan gaskiya.

Lamus ya rasu ne a ranar Talata 25 ga watan Oktoban shekarar 2022.

Ibrahim Addra, babban sakataren watsa labarai na gwamnan Nasarawa ne ya tabbatar da rasuwar Mr Lamus, kamar yadda Sahara Reporters ta rahoto.

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya halarci sallar gawar marigayin kuma ya tafi har makarbata aka birne shi a gidansa na gaskiya, rahoton Independent.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164