Ba Ta So Ta Wanke Kayanta: Magidanci Ya Yi Bidiyon Matarsa Tana Sharban Kuka a Gida

Ba Ta So Ta Wanke Kayanta: Magidanci Ya Yi Bidiyon Matarsa Tana Sharban Kuka a Gida

  • Dan Najeriya ya wallafa wani mai nan dariya na matarsa da ya saka kuka bayan ya bukaci ta yi wankin kaya
  • A wani bidiyo da yadu a TikTok, an gano matashiyar tana kuka wiwi yayin da mijinta ke mata bidiyo
  • Da suke martani ga bidiyon, wasu mutane sun yi ikirarin cewa ku kan karya takeyi yayin da abun ya ba wasu dariya

Wata mata yar Najeriya ta fashe da kuka bayan mijinta ya nemi ta wanka kayanta a gida.

A wani bidiyo da ya yadu, an gano matar tana kuka yayin da mijin ya umurceta da ya fita waje ta wanke kayanta masu datti.

Matashiya na kuka
Ba Ta So Ta Wanke Kayanta: Magidanci Ya Yi Bidiyon Matarsa Tana Sharban Kuka a Gida Hoto: @zamanie101/TikTok
Asali: UGC

Mijin wanda ya cika da mamaki ya dauki bidiyon matar tana kuka sannan ya wallafa shi a TikTok don kowa ya gani.

Yayin da yake wallafa bidiyon, ya ce:

Kara karanta wannan

Kwana ta kwanaye: Bidiyon 'yar Arewa ya girgiza intanet, ta taka leda fiye da yadda maza ke yi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Bata son wanke kayanta. Me yasa yan auta suke yin haka?”

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

@joyleo715 ya ce:

“Baka bata kudin kitson bakin Kirsimeti bane ka daina wayancewa mun gane.”

@emmydine26 ya rubuta:

“Wannan kukan farin ciki ne ta tuna yadda kake tafiyar da ita.”

@ceejay_142 ya yi martani:

“Idan ta fito waje yanzu za ta dunga daukar kanta babbar yarinya. Ji katon bakinta.”

@kenechi1 ta ce:

“Hahhahhaha a wannan sanyin. Dan Allah ka barta ta yanke shawara hahhahahhaha.”

@queenchizzy72 ta kara da cewa:

“Yi masu ta yan auta.”

Budurwa ta raba gari da saurayinta bayan mahaifiyarsa ta saka ta wanke-wanke

A wani labarin, wata matashiyar budurwa ta datse igiyar soyayyar da ke tsakaninta da saurayinta bayan ta kai ziyara gidan masu shirin zama surukanta.

Kara karanta wannan

An Yi Girman Banza: Bidiyon Yadda Matashi Ya Rusa Kuka da Hawaye Saboda Budurwarsa Tace Su Rabu

Da isarta gidan, sai mahaifiyar saurayin ta tambayeta ko ta iya abinci inda dole ta shiga kicin ta tayata girki.

Sai dai kuma, bayan sun gama cin abincin mahaifiyar saurayim ta kuma saka ta wanke-wanken kwanukan da suka yi amfani da shi.

Fargabar abun da zai faru a gaba idan aka ce ta zama surukar dattijuwar shine ya saka ta datse igiyar soyayyar da ke tsanakinsu.

Yayin da wasu suka goyi bayan abun da ta aikata, wasu na ganin sam abun da ta aikata ba daidai bane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng