Ma’aikata Sun Bada Sharadi Kan Karin Albashi, Sun ce ba Shi Kadai Ake Bukata ba
- Kungiyoyin ‘yan kasuwa da ‘yan kwadago sun yi magana a kan karin albashin da ake cewa za ayi
- Wani jagora a kungiyar NLC ya ce dole a fara duba tsadar rayuwa da karyewar da Naira take yi
- Sakataren TUC ya bada makamanciyar wannan shawara, ya ce N30, 000 da ake biya ya yi kadan
Abuja - Kungiyoyin ‘yan kwadago na kasa watau NLC da TUC ta ‘yan kasuwa ta jero sharuda a game da karin albashin da ake shirin yi a Najeriya.
Punch ta rahoto kungiyoyin su na cewa ya zama wajibi a duba matsalar tashin farashin kaya da karyewar Naira kafin gwamnati tayi karin kudi.
‘Yan kwadagon sun ce farashin kusan komai tashi yake yi a kasar nan, idan aka cigaba da tafiya a haka, babu karin da zai iya biya bukatun ma’aikata.
Mataimakin shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero ya shaidawa jaridar cewa N30, 000 ba zai isa a saye kananzir, man fetur da gas na tsawon wata daya ba.
Komai ya kara kudi a yau - NLC
"Maganar da ake yi, farashin kananzir, litar man fetur da gas da za a saya a kwanaki 30 ya fi karfin mafi karancin albashin N30, 000 da ake biya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Saboda haka ba maganar adadin kudin da za a biya ba ne, ko nawa za a bada ba zai iya magance matsalar mu ba, dole a duba tashin farashin kaya.
Idan ba haka ba kuwa, a kwana ko biyu, duka kudin za su kare." - Joe Ajaero
Abin da ya kamata gwamnati ta duba - TUC
Ajaero ya ce ba za a iya fadan nawa ya kamata a biya ma’aikatan ba, sai kwamitocin da abin ya shafa sun zauna, sun duba halin tattalin arzikin kasa tukun.
Kwamitin ya kunshi ‘yan kwadago, ma’aikata da bangaren gwamnati da suke da ta-cewa a lamarin, sai dukkaninsu su na nan sannan za a tsaida magana.
Shi ma Sakatare Janar na TUC, Nuhu Toro ya ce ana bukatar gwamnati ta tsoma baki a kan farashin kaya a Najeriya, sannan a duba yadda Naira take karyewa.
An rahoto Nuhu Toro yana cewa karin albashi kadai ba zai isa ba, ya bada misali da ya nuna ko a kudin mota, N30, 000 din da ake biyan ma’aikata za su kare.
A karshe babu kudin kiwon lafiya, abinci da kuma kula da yara, Toro ya ce ba za su bari a tafi a haka ba, a matsayinta na kungiya, TUC za ta sa baki a lamarin.
Za a kara albashi a 2023?
NLC da TUC sun yi magana ne bayan jin labarin Dr. Chris Ngige yana cewa ma’aikata da jami’an gwamnatin tarayya su saurari karin albashin da za ayi a badi.
Da ya zanta da manema labarai, Ministan kwadago da samar da aikin yi a Najeriya ya yi magana karir albashi da kudin ASUU na watanni 8 da aka ki biya.
Ngige ya kira 2022 da shekarar rigima da ‘yan kwadago ganin tataburzarsu da malaman jami’a.
Asali: Legit.ng