Za'a Rataye Wani Mutumi Bisa Gunduwa-Gunduwa da Kishiyar Mamarsa a Kano

Za'a Rataye Wani Mutumi Bisa Gunduwa-Gunduwa da Kishiyar Mamarsa a Kano

  • Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan Sagir Wada, wanda ya kashe matar babansa a jihar Kano
  • Tun shakaru Takwas da suka gabata aka gurfanar da mutumin a gaban babbar Kotun Kano kan tuhumar gunduwa-gunduwa da matar babansa
  • Lauyan dake kare wanda ake zargi yace zasu zauna su yi nazari kan hukuncin kotu kafin daga bisani su ɗauki mataki na gaba

Kano - Babbar Kotun jihar Kano mai zama a Sakatariyar Audo Bako, ta yanke wa wani mutumi, Sagiru Wada, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kama shi da laifin kisan matar babansa.

Jaridar Daily Trust ta ce Alkalin Kotun mai shari'a Aisha Mahmud, ta yanke masa hukuncin ne bayan nazari kan dukkan batutuwan dake ƙunshe a cikin Kes ɗin.

Gudumar Kotu.
Za'a Rataye Wani Mutumi Bisa Gunduwa-Gunduwa da Kishiyar Mamarsa a Kano Hoto: punchng
Asali: Twitter

Bayan dogon Nazarin, Alkalin tace ta kama Wada da laifin halaka matar babansa ta hanyar datsa ta gunduwa-gunduwa karkashin sashi na 221 na kundin dokokin Fenal Code, Kano.

Kara karanta wannan

Kano: Masu Laifi 2,260 Suka Shiga Hannun Hisba, Ta Kwashe Almajirai 1,269 Tare da Tarwatsa Motocin Giya 25

Mai shari'a Aisha Mahmud tace ta gamsu da dukkan shaidun da aka gabatar a gaban Kotu, inda ta bayyana cewa bangaren masu kara sun tabbatar da aikata laifin ba bu tababa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda shari'ar ta gudana

Legit.ng Hausa ta gano cewa an gurfanar da Sagir Wada a gaban Kotu ne shekaru Takwas da suka gabata bisa tuhumar kashe kishiyar mahaifiyarsa, Zainab Dan-Azumi, da wuka.

Lauyan dake kare wanda ake zargi, Barista Rabiu Abubakar, ya shaida wa Kotu cewa Sagir Wada na fama da taɓin hankali amma Kotun ta yi fatali da zancen saboda shaidun da aka gabatar.

Haka zalika lauyan mai ƙara, Barista Tijjani Ibrahim yace Kotu ta nazarci yadda Kes din ke tafiya cikin nutsuwa kuma babu wata hujja da ta tabbatar wanda ake zargi na da tabin hankali.

A halin yanzu, lauyan dake kare wanda ake tuhuma ya ce zasu yi nazari kan hukuncin da Kotu ta yanke kuma su ɗauki mataki na gaba.

Kara karanta wannan

AbdulJabbar: Yan Shi'a Sun Kai Karar Gwamnatin Kano Wajen Majalisar Dinkin Duniya

A wani labarin kuma Wata Matsala Ta Kunno Kai a Zaman Shari'ar Dan China Wanda Ya Kashe Ummita a Kano

A kwanakin baya kunce cewa wata sabuwar matsala ta haddasa ɗage shari'ar kisan Ummita, budurwa yar Kano da wani Ɗan China ya kashe.

Lamarin dai ya kai ga tiƙasata Kotu ta sanar da ɗage zaman zuwa wata na gaba don shawo kan komai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262