Matar Fitaccen Jigon APC A Legas Ta Mutu Ba Zato Ba Tsammani

Matar Fitaccen Jigon APC A Legas Ta Mutu Ba Zato Ba Tsammani

  • Iyalan Honarabul Dayo Bush-Alebiosu, tsohon dan majalisar wakilai suna zaman makoki, kwanaki kadan kafin karshen shekarar 2022
  • Hakan na zuwa ne yayin da fitaccen jigon jam'iyyar APC a Legas ya rasa matarsa a ranar Talata 27 ga watan Disamba
  • Iyalan sun tabbatar da rasuwar ta cikin wani sanarwa da suka fitar, inda suka ce Yetunde Alebiosu, nee Sotomi ta rasu tana shekara 48

Wani rahoto da PM News ta fitar ya ce Yetunde, matar fitaccen jigon jam'iyyar APC a Legas kuma tsohon dan majalisar wakilai, Dayo Bush-Alebiosu, ta rasu ta zato ba tsammani.

Hon Dayo Bush-Alebiosu tsohon dan majalisar wakilai na tarayya ne mai wakiltar mazabar Kosofe a Legas.

Matar jigon APC
Matar Fitaccen Jigon APC A Legas Ta Mutu Ba Zato Ba Tsammani. Hoto: Yeye Bush-Alebiosu.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da motoci biyu suka yi karo, mutum 1 ya hallaka, yawa sun jikkata

Menene ainihin abin da ya faru?

Yetunde ta rasu a ranar Talata, 27 ga watan Disamban 2022, a cewar iyalan.

Sanarwar da iyalan Alebiosu suka fitar a ranar Laraba 28 ga watan Disamba ya ce marigayiyar, nee Sotomi, kafin rasuwarta mataimakiyar direkta ne a Ma'aikatar Shari'a na Jihar Legas, jaridar The Sun ta rahoto.

Iyalanta sun tabbatar da rasuwarta, sunyi karin bayani

Sanarwar ta ce ta rasu a wani asibiti mai zaman kansa da ke Legas misalin karfe 4 na yammacin ranar Talata 27 ga watan Disamban 2022.

Matar tsohon dan majalisar ta rasu tana da shekaru 48.

Sanarwar ta ce:

"Cikin alhini kuma da godiya ga Allah muna sanar da rasuwar matarmu kuma mahaifiya da muke kauna."

An haife ta ne a ranar 13 ga watan Satumban 1974, a gidan su marigayi Birgediya Janar Folusho Sotomi.

Jigon jam'iyyar APC Ya Mutu A Hatsarin Mota A Jalingo

Kara karanta wannan

Shahararren Dan Takarar Gwamnan APC Ya Dage Kamfen Dinsa, Ya Bada Dalili

Rahoton da Tribune ta rahoto ya bayyana cewa Hon. Abdullahi Kanti, shugaban kwamitin kamfen din dan takarar gwamna na jam'iyyar All Progress Congress, APC, a karamar hukumar Karim Lamido, ya riga mu gidan gaskiya.

Kanti ya rasu ne a wani mummunan hadarin mota da ya faru a ranar Talata 27 ga watan Disambar 2022 a kan hanyar Lau Road zuwa Jalingo a jihar Taraba.

Sanata Emmanuel Bwacha, dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Taraba ya mika ta'azziya ga iyalan marigayin, yana mai cewa ya rasa mutumin kirki mai son zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164