Shahararren Dan Takarar Gwamnan APC Ya Dage Kamfen Dinsa, Ya Bada Dalili

Shahararren Dan Takarar Gwamnan APC Ya Dage Kamfen Dinsa, Ya Bada Dalili

  • Sanata Bassey Otu ya sanar da dakatar da dukkan harkokin kamfen dinsa har sai baba ta gani
  • Ya yanke wannan shawarar ne awanni bayan hatsarin da ya faru wurin bikin Calabar Festival da ya yi sanadin rasuwar mutum 7 sannan wasu 29 suka jikkata
  • A sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, 28 ga watan Disamba, Sanata Otu ya bayyana cewa ya dakatar da kamfen dinsa ne don karrama wadanda abin ya shafa

Cross Rivers, Calabar - Dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Cross Rivers Sanata Bassey Otu ya dakatar da kamfen dinsa.

Kamar yadda PM News ta rahoto, mutuwar mutane bakwai a wurin bikin Calabar Carnival da ya faru a ranar Talata 27 ga watan Disamba ne yasa ya dauki wannan matakin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Halaka Jigon Jam'iyyar PDP A Gidan Mahaifinsa

Bassey Otu
Shahararren Dan Takarar Gwamnan APC Ya Dage Kamfen Dinsa, Ya Bada Dalili. Hoto: Bassey Otu.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cikin sanarwa mai dauke da sa hannun Sanata Otu a Calabar a ranar Laraba, 28 ga watan Disamba, ya bayyana cewa ya yanke shawarar dakatar da kamfen dinsa ne don karrama mutane bakwai da suka mutu a wurin taron da saura 29 da suka jikkata.

Sanarwar ta ce:

"Labarin bakin ciki na mutuwar wasu mazauna jihar Cross Rivers wadanda suka bar gidajensu don kallon faretin masu babura ya girgiza ni.
"Ina mika ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayyukansu kuma ina addu'a Allah ya basu hakurin jure rashin."

Dan takarar na APC a jihar Cross Rivers ya soki afkuwar lamarin yana mai cewa 'lamari na da ya kamata a kiyayye faruwarsa.'

Ya yi kira ga gwamnatin jihar da mazauna garin su yi aiki tare don yin bincike ta gano wadanda ke da hannu a lamarin, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zamfara: "Dan Takara Ya Ziyarci Farar Hula da Luguden Soja ya Ritsa Dasu a Zamfara, Ya Basu Makuden Kudi

Sanata Otu ya kare da cewa:

"Don karrama wadanda suka mutu, na yanke shawarar dakatar da dukkan abubuwan siyasa na har sai baba ta gani don yin zaman makoki tare da iyalan wadanda suka rasu da wadanda suka jikkata."

A cewar kididdiga daga hukumar kiyayye haddura na kasa, FRSC, ya ce wadanda abin ya shafa sun hada da maza 21, mata uku, yara maza biyu da yara mata uku.

Chimaroke Nnamani ya ce Bola Tinubu ne zai lashe zaben shugaban kasa na 2023

Sanata Chimaroke Nnamani, tsohon gwamnan jihar Enugu ya ce Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar gwamna na jam'iyyar APC ne zai lashe zaben shugaban kasa na 2023.

Sanatan mai wakiltar mazabar Enugu-East ya bayyana hakan ne yayin da mambobin kwamitin yakin zaben shugaban kasa suka ziyarce shi a garinsa na Agbani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164