Kada Ka Kuskura Ka Shekara 10 Da Mata 1: Malam Daurawa Ya Shawarci Maza

Kada Ka Kuskura Ka Shekara 10 Da Mata 1: Malam Daurawa Ya Shawarci Maza

  • Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, babban malamin nan na musulunci ya shawarci maza masu ra'ayin kara aure
  • Daurawa ya shawarci maza da ke da burin kara aure da kada su yarda su yi shekaru 10 da mace daya ba tare da sun yi karin ba
  • A cewar Shehin malamin da zaran mutum ya yarda diyarsa ta zama budurwa kafin ya kara aure toh ita ce zata zamo abokiyar rigimar amaryar tasa

Shahararren malamin nan na addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayar da muhimman shawarwari ga maza a kan zamantakewar aure.

Daurawa ya shawarci maza da ke da muradin son kara aure a rayuwarsu da kada su kuskura su haura shekaru 10 da mace daya.

Daurawa
Kada Ka Kuskura Ka Shekara 10 Da Mata 1: Malam Daurawa Ya Shawarci Maza Hoto: Mal.Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

Jaridar Aminiya ta rahoto cewa a hirarsa da Freedom Radiyo Kano, malamin musuluncin ya ce idan idan har namiji ya shafe yawan wannan shekaru da mace guda, toh lallai lokaci ya kure masa.

Kara karanta wannan

Masana Sun Gano PrEP Kan Iya Taimakawa Mutuka Gaya Wajen Kare Kamuwa Da Cutar 'Kanjamau

Sheikh Daurawa ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Kada ka haura shekaru 10 ba tare da ka kara aure ba idan har kana da muradin aikata haka. Idan ka haura shekaru 10 akalla kana da diya 'yar shekara takwas ko tara.
“Da zarar diyarka ta kai shekara 15 ba ka kara aure ba, to wacce zaka auro da wuya ta wuce shekara 20. Za ka ga tsakaninsu da diyar taka bai wuce ’yan tazarar shekaru ba.
“Ka ga kenan matarka ta samu abokiyar fada. Akwai wacce za ta iya tura diyarta ta samu amarya su rika fada ko ta yi ta dukan amaryar saboda ta fi ta karfi.
"Da haka ne nake kira ga wanda ke son karin aure ya shirya da wuri, kuma kada ka yarda duk dadin miyar mace ka furta cewa ba za ka kara aure ba."

Kara karanta wannan

Ka latsa ni: Kyakkyawar budurwa ta tari wani dan Najeriya, ta nemi su fara soyayya

Hukuncin maganin mata

A wani labarin kuma, malamin addinin ya magantu a kan hukuncin da ke tattare da amfani da magungunan mata da karin girman mazaunai da mama.

Da ya zanta da gidan rediyon Freedom da ke garin Kano, Daurawa ya ce idan har magungunan gyara jiki ne mace za ta sha wadanda basu da illa don kada yanayin jikinta ya sauya, ta yadda mijinta ba zai kyamaceta ba babu laifi.

Sai dai ya ce magungunan da ake zuwa karbowa wurin boka da matsafa haramun ne domin a cewarsa wasu a kan nemi mace ta hada da jinin al'ada ko ayi rubutu a ce ayi tsarki da shi da dai sauransu.

Manomi mai yara 102 ya ce baya son karin haihuwa

A gefe guda, Legit.ng ta rahoto a baya cewa wani tsoho mai suna Musa Hasahya, wanda ke zama a Lusaka, Uganda, ya bayyana cewa yanzu baya so ko mutum daya daga cikin matansa 12 ta kara haihuwa.

Manomin wanda ke da 102 da jikoki 568 ya ce yana fama da yadda zai ciyar da iyalinsa a yanzu haka domin karfinsa ya fara karewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng