Niger: Sabon Hatsarin Mota ya Halaka 'Yan Sanda 3 da Wasu Mutum 5
- Kasa da awannin 24 bayan aukuwar mummunan hatsarin kan titin da ya lashe rayuka 11 a karamar hukumar Mokwa a Neja, wani hatsarin ya sake aukuwa a yankin Gunu na jihar
- Hatsarin ya lashe rayukan mutane takwas duk da 'yan sanda uku, wanda ya auku kan titin Minna zuwa Gwada a daren Talata
- Ganau ya bayyana yadda lamarin ya auku tsakanin mota kirar Toyota Camry da Volkswagen, inda ya shafi mutane 12, takwas daga ciki suka mutu nan take
Neja - A kasa da awa 24 bayan hatsarin mota a titi ya lashe rayuka 11 a karamar hukumar Mokwa na jihar Neja, wani mummunan hatsarin ya sake aukuwa a yankin Gunu na jihar, wanda rayukan mutane takwas suka salwanta duk da 'yan sanda uku, jaridar Leadership ta rahoto.
Ganau ya bayyana yadda hatsarin ya auku a daren Talata kan titin Minna zuwa Gwada, wanda ya shafi motoci biyu - mota kirar Toyota Camry da motar kirar Volkswagen Wagon.
Haka zalika, bincike ya bayyana yadda hatsarin ya ritsa da mutane 12, inda aka tabbatar da rasuwar takwas yayin da hudu suka samu raunuka gami da garzayawa dasu babban asibitin Minna, babban birnin jihar.
Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, kwamanda hukumar kiyaye hadurran a tituna na shiyyar, Kumar Tsukwam ya bayyana, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da alakanta shi da tsabar gudu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yace wadanda suka samu raunikan an kai su asibiti mafi kusa yayin da mamatan aka adana gawawwakinsu a ma'adanar gawawwaki dake babban asibitin Minna.
Motoci biyu sun yi karo, mutum 1 ya mutu wasu sun jigata
A wani labari na daban, direban mota a jihar Anambra ya rasa ransa, yayin da wasu mutum takwas sun jigata a wani gagarumin hatsarin mota da ya auku a mahadar Uko kusa babban titin Onitsha-Nteje-Awka dake jihar Anambra.
Motar mai kirar Toyota/Hiace bas mai lambar mota JVR 616 XA ta 'yan kasuwa ne ta ci karo da wata motar kirar bas mai lamba JJJ 179 XS a ranar laraba.
Motocin suna dauko mutane 14; maza 4 manya da mata 6 manya sai kananan yara maza da mata wadanda 5 daga cikinsu sun kubuta babu rauni.
Asali: Legit.ng