Qatar Za Ta Ba da Kyautar Motoci Bas da Aka Yi Amfani da Su a Gasar Kofin Duniya Ga Labanon

Qatar Za Ta Ba da Kyautar Motoci Bas da Aka Yi Amfani da Su a Gasar Kofin Duniya Ga Labanon

  • Bayan kammala wasan cin kofin duniya, kasar Qatar za ta yiwa kasar Lebanon alheri mai girman gaske
  • Qatar ta sanar da cewa, za ta ba da kyautar kayayyaki da yawa da aka yi amfani dasu a wasannin da aka gudanar
  • Qatar ta nemi a sake ba ta damar karbar bakuncin wasannin Olympic da za a gudanar nan da shekaru 12 masu zuwa

Lebanon - Jim kadan bayan kammala wasan cin kofin duniya, kasar Qatar ta ce za ta yi kyautar motocin da aka yi amfani dasu wajen jigilar fasinja a lokacin wasannin, BBC Hausa ta ruwaito.

Qatar ta ce za ta ba kasar Lebanon kyautar motocin ne domin ba da gudunmawa ga inganta harkar sufuri a kasar, kamar yadda rahotanni daga kasar ta Lebanon suka bayyana.

Idan baku manta ba, kasar Qatar ne ta samu damar daukar nauyi tare da karbar bakuncin kasashen duniya a gasar cin kofin duniya da aka gudanar na wannan shekarar da ke gargarar karewa.

Kara karanta wannan

An Suburbudi Wani Mutumin Da Yaje Sayen Abinci Da Sabon Naira, Bidiyo

Qatar za ta ba Lebanon kyautar motoci bas
Qatar Za Ta Ba da Kyautar Motoci Bas da Aka Yi Amfani da Su a Gasar Kofin Duniya Ga Labanon | Hoto: dohanews.co
Asali: UGC

Firaministan kasar Najib Mikati, an ce ya zanta da jami’an kasar Qatar domin samun wadannan motoci bayan kammala wasan cin kofin duniya mai dimbin tarihi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A tun farko, kasar Qatar ta ce za ta yi kyautar kayayyaki da yawa da aka yi amfani dasu a wasannin, kuma za ta ba da su ne ga kasashe masu tasowa.

Kayayyakin da Qatar za ta kyautar

Kadan daga abubuwan da kasar tace za ta ba dasu kyauta sun hada da;

  1. Manyan filayen wasanni
  2. Kujerun cikin filayen wasannin
  3. Motoci sama da 1,000 da dai sauran kayayyaki masu daraja

Ba sabon abu bane samun karimci daga kasashen Larabawa masu dimbin dukiya kamar kasar Qatar.

A tun farko, kasar Qatar ta siya sabbin motocin bas sama da 3,000 baya ga 1,000 da kasar ke dashi tun kafin fara wasannin cin kofin duniya, rahoton Doha News.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari na Kokarin Dawo da Harajin da Isa Pantami Ya Hana a Kakaba a 2022

Sai dai, da majiya ta tuntubi gwamnatin kasar Qatar, har yanzu bata samu bayani daga gwamnati ba kan wannan yunkuri da Lebanon ta yi ikrari a kansa.

Bayan kammala wasannin cin kofin duniya, kasar Qatar ta nemi a ba ta damar sake daukar nauyi da karbar bakuncin wasannin Olympic a nan gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel