Rashin Biyan Haraji: 'Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 4, Sun Sace Sama da Manoma 100 a Neja

Rashin Biyan Haraji: 'Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 4, Sun Sace Sama da Manoma 100 a Neja

  • A kalla manoma hudu sun rasa ransu yayin da masu garkuwa da mutane suka sace sama da mutane 100 duk da mata da yara a kananan hukumomin Rafi da Mashegu
  • Hakan ya biyo bayan harajin da 'yan bindiga suka sanya wa wasu yankuna na N3 miliyan a matsayin sharadin daina garkuwa da mutane tare da barinsu girbin amfanin gonarsu
  • Baya ga kananan hukumomin biyun, 'yan bindigan suka auka yankunan Gidogori, Pandogari, da Durumi makonni biyu da suka shude gami da kisa da sace mutane da dama

Neja - 'Yan bindiga sun halaka a kalla manoma hudu gami da yin garkuwa da 100 suka da mata da yara daga yankuna 14 a Mashegu da kamar hukumar Rafi na jihar Neja a makonni uku da suka wuce.

Taswirar Neja
Rashin Biyan Haraji: 'Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 4, Sun Sace Sama da Manoma 100 a Neja. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Daily Trust ta tattaro yadda aka yi garkuwa da sama da rabin manoman yayin girbin masara, wake, dawa da waken soya a gonakinsu.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Bayyana Abu 1 Da Yan Kaduna Ba Za Su Taba Manta El-Rufai a Kansa Ba

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wadanda aka halaka sun hada da sarkin garin, 'yan sa kai biyu da wani mutum daya yayin farmakin a karamar hukumar Mashegu.

Majiyoyi sun labarta yadda yankunan da aka hara suka hada da Sabon - Rijiya, Tsohon-Rami, Bakwai-Bakwai, Mulo, Kawo-Mulo, Nasarawa-Mulo, Mai- Azara, Foje, Mutum-Daya, Beji, Gidan-Malam, Bokuta, Chetaku da Gbazhi, hakan ya tilasta mazauna yankin tserewa zuwa anguwar Ibbi da sauran wuraren da suka samun tsaro a karamar hukumar.

A karamar hukumar Rafi da yankunan Shiroro, an ruwaito yadda aka sace wasu manoma 61 a yankin Gidogori, Pandogari da Durumi a makonni biyu da suka shude.

Mazaunan sun bayyana yadda 'yan bindiga suka sanya N3 miliyan matsayin kudin haraji ga ko wanne yanki a matsayin dokar daina garkuwa da mutane da kuma barinsu girbin amfanin gonarsu, wanda yanki daya ne kadai ta iya biya. 'Yan bindiga sun fara satar kayan abincin da suka girbe.

Kara karanta wannan

Rayuka 15 Sun Salwanat Sakamakon Harin 'Yan Ta'adda a Sokoto da Zamfara, Wasu 8 Sun Jigata

Wasu mazauna yankin, Muhammad Sanusi da Abdulrahman Inuwa, sun bayyanawa Daily Trust yadda barayin suka bindige wani 'dan sa kai mai suna Abubakar ya rasa ransa bayan 'yan bindiga sun sace shi a ranar Alhamis.

'Yan ta'addan sun kai hari Mulo, sa anguwannin dake makwabtaka, inda suka kashe sarkin Mulo, Alhaji Usman Garba wanda hakan ya tilasta mazauna Fage da Mulo tserewa daga gidajensu.

A zantawar da Legit.ng Hausa tayi da Abdulkarim Pandogari, wanda aka fi sani da Abdul, ya sanar da cewa farmakin 'yan bindiga ya dade yana addabar yankunansu.

A cewarsa, sai da suka hada wasu kudade wadanda bai bayyana ko nawa bane domin su kubuta daga sharrin 'yan bindiga don su girbe kayan abincinsu hankali kwance.

"Tabbas an sace wasu manoma har a yankinmu amma duk saboda matsalar haraji ce. Mun hada musu wasu kudi amma ba duka yankunan aka hada ba."

- Yace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng