Bidiyon Wata Yarinya Tana Kurbe Lemun Kwalba Ta Tada Kura a Intanet, Jama’a Sun Yi Ca a Kai
- Wata yarinya ‘yar Najeriya ta nuna shiga jin dadi yayin da ta kurbi lemun kwalba; Fanta, jama’a sun yi martani a kafar sada zumunta
- Yayin da take kurbar lemun, yarinyar ta ce ta shiga annashuwa kuma tana wasanta ba kamar sauran mutane ba
- Daga cikin wadanda suka yi martani har da wadanda suka ce sam yarinyar bata san ya ake samo kudi ba, shi yasa take haka
Wata kyakkyawar yarinya da ta sanu a kafar sada zumunta ta jawo cece-kuce a kafar TikTok yayin da ta nuna lokacin da take shan lemun kwalba mai sanyi.
A bidiyon da aka yada, yarinyar mai hakora kyawawa ta shaidawa duniya tana jin dadinta yadda ta ga dama.
Ta fada a bidiyon cewa:
“Dadi na son kashe ni. Wasa kawai nake.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jama’ar TikTok da yawa ne suka yi martani kan wannan yarinyar da aka gani tana sharholiya da lemun kwalba.
Kalli bidiyon:
Martanin jama’a
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, akalla mutum 500 ne suka yi martani kan bidiyon, mutum 37,000 sun yi dangwalen nuna sha’awarsu a kai.
Ga kadan daga martanin da muka tattaro muku:
gloriaandrew33:
"Ki yi wasanki, an kusa komawa makaranta.”
Brighton:
"Kamar wannan Fatan akwai barasa a ciki.”
tessyabbey7:
"Me yasa ba za ki ji dadinki ba, kina biyan kudin haya ne ko kina siyan abinci??”
Umusumayyah1:
"To ai baki da damuwa ko daya, babu batun siyan wani abu wasa ne abin da dace masiyiya.”
Ramorney:
"Muryar ta min kama da ta pawpaw.”
ladypatra7:
"Yarinya ki ji dadinki an kusa dawowa makaranta nan kusa.”
Edmund favour:
"Ina son irin wadannan hakoran nata, ina son yarinyar nan.”
Shakone Tracey:
"Kawai kada ki damu, ba ki sayen komai, baki siyan abinci, kuka kike idan kina jin yunwa.”
Yaro ya kurbi barasar mahaifinsa
A wani labarin kuma, wani yaro ne ya samu barasar da mahaifinsa ke sha, ya buya ya fara kwankwade ta.
Bayan kama shi hannu dumu-dumu, mahaifin nasa ya titsiye shi a cikin gida, yana tuhumar dalilin da yasa ya sha bararasar.
Jama'ar kafar sada zumunta sun yi martani, sun ce ai ba laifin yaron bane, na mahaifin ne.
Asali: Legit.ng