Tattalin Arzikina Na Kara Yin Kasa: Manomi Mai Mata 12 Da Yara 102 Na Duba Yiwuwar Daina Haihuwa
- Duk da kasancewarsa manomi Musa Hasahya mai shekaru 67 yana da matan aure 12, yara 102 da kuma jikoki 568
- Magidancin na rayuwa da iyalinsa a yankin Lusaka da ke kasar Uganda inda aka halasta auren mata da yawa
- Matansa sun fara amfani da kwayoyin hana daukar ciki don hana kansu ci gaba da haihuwar 'ya'ya saboda tsadar rayuwa
Uganda - Wani manomi a kasar Uganda da ke da yara 102 da jikoki 568 da ya samu daga matansa 12 ya yanke shawarar daina haihuwa.
Musa Hasahya mai shekaru 67 a duniya ya bukaci matansa da su fara amfani da magungunan hana daukar ciki don su samu su dunga cin abinci.
Jaridar The Sun ta nakalto Musa yana cewa:
"Kudaden shigana na kara yin kasa a yan shekarun nan saboda tsadar rayuwa kuma iyalina na kara habbaka.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ina ta auren mata daya bayan daya. Ta yaya namiji zai gamsu da mace daya.
"Dukka matana na zaune ne tare a gida daya.
"Ya fi mun saukin lura da su da kuma hana su hulda da sauran maza a kauyen nan."
Na fara shan kwayoyin hana daukar ciki, amaryar Musa
Amaryarsa mai suna Zulaika wacce ta haifa masa yara 11 ta ce:
"Ba zan sake haihuwar 'ya'ya ba. Na ga mummunan yanayi na rashin kudi kuma yanzu ina shan maganin hana daukar ciki."
Musa da iyalinsa na zama a Lusaka da ke kasar Uganda inda aka halasta auren mata da yawa.
Sai dai kuma akwai takaddama sosai game da shan kwayoyin hana daukar ciki kuma a kan alakanta shi da lalata.
Kimanin kaso uku na yaran Musa suna rayuwa da shi ne a gonarsa.
Shekarun dan autansa shida sannan dansa na fari yana da shekaru 51 wanda ya girmi amaryarsa Zulaika da shekaru 21, rahoton DailyMail.
Yanzu baya iya aiki saboda rashin lafiya kuma biyu daga cikin matansa sun rabu da shi saboda matsalar rashin kudi.
Ana tsaka da daurin aure, amarya ta ce bata yi
A wani labarin kuma, mun ji cewa wata amarya ta hau sama ta duro tace baya auren mijinta a daidai lokacin da limami ke shirin daura masu aure a coci.
Asali: Legit.ng