Kaduna: 'Yan Sanda Sun Damke Dillalin Makamai, An Samo Kaya Masu Hatsari
- Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta bayyana yadda jami'anta na yankin Tudun wada Zaria suka yi nasarar cafke wani da ake zargin 'dan bindiga ne
- An kama wanda ake zargin mai suna Bilyaminu Saidu 'dan shekaru 33 da bindiga kirar AK47 guda daya, carbin da harsasai 344 da babur
- Kakakin rundunar ya bayyana yadda ake cigaba da bincike da sa ran zakulo sauran tawagar 'yan bindigar ba tare da jinkiri ba
Kaduna - Rundunar 'yan sandan jihar ta bayyana yadda jami'anta suka cafke wani gawurtaccen 'dan bindiga a jihar, jaridar Premium Times ta rahoto.
Haka zalika, rundunar ta bayyana yadda ta gano bindigu hudu kirar AK47, carbin harsasai 344 da babur guda daya.
Kakakin 'yan sandan jihar, Muhammad Jalige ne ya tabbatar da kamen a wata takarda da ta fita ranar Lahadi a Kaduna.
Jalige ya ce jajircewa da sabbin dabarbarun jami'an da dakarun rundunar ne wajen tabbatar da sun bi dokoki tsare anguwanni yayin gudanar da bukukuwan lokacin ne ya haifar da sakamako mai kyau.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewarsa:
"A ranar 23 ga watan Disamba, misalin karfe 5:30, jami'an da ke aiki a Tudun wada Zaria, yayin sintiri a Kwarkwaran Manu, anguwar Basawan garin Zaria, suka yi ram da wasu mutane biyu da babura marasa rijista tare da jakunkuna rufaffu a wani yanayi rashin gaskiya kan babur.
"Yayin da aka dakatar da su don bincikarsu, fasinjar kan babur din ya dira gami da tserewa, ta hanyar tsawaita zargin a idon jami'an.
"Babur din da matukin, wanda ya bayyana kansa a matsayin wani Bilyaminu Saidu mai shekaru 33 daga kauyen Shuwaku na karamar hukumar Bakori na jihar Katsina, wanda cikin hanzari aka bincikesa tsaf gami da yin ram da shi.
"Abubuwan da aka kamashi fasu sun hada da bindigu hudu kirar AK47, carbin harsasai 344 masu girman 6.62mm, wayoyi da layu."
Jaridar The Cable ta rahoto cewa, Jalige ya ce an kama wanda ake zargin, binciken da aka yi ya bayyana yadda shi da wanda ya gudu suke kan hanyarsu na kai wa tawagarsu miyagun makaman.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Yekini Ayoku yayi umarni da tsananta bincike don bankado tushen da inda za su kai miyagun makaman tare da kama hatsabiban da ake zargi.
'Yan sanda sun kai mutum 9 gaban Kotu kan zargin kaiwa Atiku Hari a Borno
A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Borno ta tabbatar da cafke wasu mutum tara tare da gurfanar dasu kan zargin kaiwa tawagar Atiku hari a jihar Borno.
Asali: Legit.ng