Kiriku: Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ka Sani Game Da Dan Barkwanci Mafi Karancin Shekaru a Najeriya
- Dan wasan barkwanci, Kiriku, ya shiga jerin shahrarrun yan wasan barkwanci a Najeriya a shekarar nan ta 2022
- Legit a kwanakin baya ta zanna da Kiriku domin tattaunawa da shi tare da iyayensa
- Dan barkwancin mai shekaru 8 da haihuwa kwanakin nan ya sayawa mahaifinsa babban mota
Yaro dan wasan barkwanci, Enorese Victor, wanda aka fi sani da Kiriku, ya zama zakaran gwajin dafi cikin masu wasan barkwanci a kafafen ra'ayi da sada zumunta.
Duk da karancin shekarunsa, dubban mutane na bibiyansa a Soshiyal Midiya kuma suna son bidiyoyin da yake yi.
Legit ta tattaro muku abubuwa 5 game da Kiriku
1. Yaushe aka haifesa
Kiriku haifaffen dan jihar Edo ne kuma shine yaro na hudu kuma dan autan gidansu. An haifeshi ranar 17 ga Disamba, 2014 a birnin BeninCity.
2. Ya fara wasan barkwanci yana dan shekara 4
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kiriku ya fara wasan barkwanci da fim a 2018 yana dan shekara 4.
Babban yayansa mai suna, Umbrella Boy, ne diraktansa kuma yake taya shi wajen shirye bidiyoyin barkwancin.
Umbrella Boy ne ya baiwa Kiriku karfin gwiwar fara barkwanci.
3. Yaushe ya shahara
Kiriku ya samu shahara ne a 2021 lokacin da shahrarren dan Instagram Tunde Ednut ya wallafa bidiyonsa a shafinsa.
Hakan ya sa dubban mabiyan Tunde Ednut suka kalli bidiyon kuma aka fara kallon bidiyonsa.
4. Dukiyoyin da ya mallaka
Kiriku ya baiwa mutane mamaki a soshiyar midiya lokacin da ya sayi motoci biyu kirar Mercedez Benz guda biyu lokaci guda.
Cikin yan watanni kadan ya sake sayen sabuwar mota wa mahaifisa.
Ana kyautata zaton cewa Kiriku da yayansa suna gab da sayan gida a unguwar Lekki ta jihar Legas.
Kwanakin baya Kiriku ya samu lambar yabo daga wajen Youtube bayan samun sama da mabiya 100,000.
5. Mabiya
Kiriku na daya daga cikin yan barkwancin da suka fi mabiya a kafafen ra'ayi da sada zumunta ta soshiyal midiya.
Kiriku na da mabiya milyan 1.3 a manhajar Instagram, mabiya 231,000 a shafin YouTube da kuma mabiyar milyan 3.4 a TikTok.
Asali: Legit.ng