Karya Ne, Ban Taba Yunkurin Kara Aure Ba - Shugaba Buhari

Karya Ne, Ban Taba Yunkurin Kara Aure Ba - Shugaba Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari bait aba yunkurin kara aure ba kamar yadda wasu yan Najeriya suka dunga yayatawa
  • Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wanda ya bayyana abun da suka tattauna da B uhari ne ya sanar da hakan a ranar Juma'a, 23 ga watan Disamba
  • Osinbajo ya nakalto Buhari yana cewa, wasu mutane sun zata da gaske zai kara yin wani auren

Abuja - Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana abun da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce game da rade-radin cewa yana shirin kara aure.

Osinbajo ya ce Buhari ya bayyana masa cewa batun ya yadu sosai a wannan lokacin kuma wasu mutane sun zata da gaske ne, rahoton The Cable.

Buhari da mukarrabansa
Karya Ne, Ban Taba Yunkurin Kara Aure Ba - Shugaba Buhari Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Facebook

A cewar mataimakin shugaban kasar, Buhari ya bayyana cewa lamarin ya kai har wasu yan Najeriya sun isa masallaci suna tsammanin cewa a nan ne za a daura auren shugaban kasar.

Kara karanta wannan

"Abin Da Ya Janyo Rasuwar Ƴaƴa Na 2", Buhari Ya Yi Magana Kan Wani Sirrinsa Mai Sosa Zuciya

Da yake nakalto jawabin shugaban kasar, Osinbajo ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wadannan mutanen kawai suna ta zarge-zarge iri-iei, suna ta shirya tatsuniyoyi, harma suna cewa ni ina shirin sake aure.
"Harma wasu wawayen mutane suka yi ta jira a babban masallacin kasa, suna jirana na zo na sake aure."

Na rasa 'ya'yana biyu saboda cutar sikila

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya magantu a kan cutar da ta kashe masa 'ya'yansa har su biyu.

A ranar Juma'a, 23 ga watan Disamba, Buhari ya bayyana cewa cutar sikila ce ta yi sanadiyar ajalin yaransa guda biyu.

Ya bayyana cewa tsohuwar matarsa da ta kwanta dama, Safinatu ita ta haifa masa yaran da suka amsa kiran Allah.

A gefe guda, shugaban kasar ya kuma yi tsokaci a kan jita-jitan da aka yi ta yadawa cewa ba shine a fadar shugaban kasa ba, wani ne mai suna Jibrin daga Sudan.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kanu, Shugaban 'Yan tada Kayar Baya ta IPOB, Yana Bukatar Aikin Zuciya, Lauyansa

Buhari ya ce sam lamarin bai masa dadi ba domin kuwa ba abun dariya bane face cin zarafi karara domin a cewarsa hakan na iya kawo karan tsaye a cikin al'umma.

Sai dai kuma shugaban kasar ya ce abun bai dame shi ba domin 'yan Najeriya sun iya kirkiro shirme kan abin da suka gaza fahimta kai tsaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng