Shugaba Buhari Ya Nada Funtua a Matsayin Babban Daraktan NigComSat

Shugaba Buhari Ya Nada Funtua a Matsayin Babban Daraktan NigComSat

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sabon nadi a hukumar sadarwar tauraron dan Adam, an nada Tukur Muhammad Funtua
  • Funtua ya kasance injiniya kuma tsohon babban ma'aikaci a kamfanoni daban-daban na kasar nan da ma kasashen waje
  • Batun nada Funtua ya fito ne daga ofishin ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nada Tukur Muhammad Funtua a matsayin Manajan Darakta a ma'aikatar sadarwar tauraron dan-adam (NIGCOMSAT).

Wannan nadin na zuwa ne bayan da tsohon manajan daraktan hukumar, Dr Abimbola Alale ya yi ritaya daga aiki.

Funtua ya kasance injiniya, kuma dan asalin jihar Katsina ne, Vanguard ta ruwaito.

An haife shi a ranar 24 ga watan Nuwamban 1966, ya karanta ilimin sinadarai a digirinsa na farko.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Najeriya Ta Bada Hutun Kirsimeti Da Sabon Shekara

Buhari ya yi sabon nadi a hukumar NigComSat
Shugaba Buhari Ya Nada Funtua a Matsayin Babban Daraktan NigComSat | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika, ya yi karatun digiri na biyu a fannin kasuwanci, kamar yadda jarida The Nation ta ruwaito.

Ayyukan da Funtua ya yi a baya

A cewar sanarwar da ma'aikatan sadarwa ta fitar ta hannun hadimin minista Isa Ali Pantami, kafin wannan matsayin da aka ba Funtua, ya kasance daraktan lafiya a ma'aikatar simintin BUA.

Hakazalika, ya yi aiki kamfanin simintin Lafarge da dai sauran manyan kamfanoni ciki har da na simintin Dangote.

Baya ga zurfi a karatu, Funtua yana kwarewa da sanin makamar aiki na sama da shekaru 30 a fannin injiniyanci, lafiya, kirkira, kariya da muhalli.

Hakazalika, kwararre ne a fannin sadarwa, kuma ya samu takardun shaida daga manyan kungiyoyin dake tantance kwarewa a gida Najeriya.

Gwamnatin Buhari ya ci gaba da nade-nade a ma'aikatu da dama don tafiyar da ayyuka yada ya kamata.

Kara karanta wannan

Ana Saura Watanni 5 ya Bar Ofis, Shugaba Buhari Ya Yi Sababbin Nade-naden Mukamai

Buhari Ya Nada Kwarrren Dan Jarida Matsayin Sabon Shugaban NTA Na Kasa

A bangare guda, shugaba Buhari ya nada Mr Salihu Dembos a matsayin sabon direkta-janarna Gidan Talabijin Na Najeriya, NTA.

Ministan Sadarwa da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan, kamar yadda wani rahoton jaridar Punch ya ruwaito.

Rahoton ya bayyana cewa, wannan nadi da aka yi babban dan jaridar na tsawon shekaru uku ne.

Mr Dembos ya kasance babban ma'aikaci a NTA a jihohin daban-daban kafin daga bisani ya samu nadin da shugaba Buhari ya yi masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.