Ina Iyakar Bakin Ƙoƙarina Amma Ƴan Najeriya Sun Raina -Shugaba Buhari
- Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya koka kan yadda ƴan Najeriya basu yabawa da ƙoƙarin da yake yi
- Shugaba Buhari yace akwai wasu ɓata gari da suka yi ƙoƙatin yiwa gwamnatin sa baƙin fenti
- Shugaban ƙasar yace ko kaɗan ba zai yi kewar barin karagar mulki ba saboda tsangwamar da ake masa
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana iyakar baƙin ƙoƙarin sa ga ƴan Najeriya amma hakan bai wadatar ba.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a daren ranar Juma'a yayin wata liyafa ta musamman da ƴan'uwa da abokan arziƙi suka haɗa masa domin murnar cikar sa shekara 80 a duniya. Jaridar The Cable ta rahoto.
Shugaban ƙasar yace akwai wasu mutane da suka yi ƙoƙarin ɓata wa gwamnatin sa suna.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Na yi amanna cewa ina iyakar baƙin ƙoƙari na, amma iyakar iyawar tawa tayi kaɗan. A cewar Buhari.
Saboda akwai mutanen da suke tunanin za su bani tsoro domin samun abinda suke so maimakon su bi hanyoyin da yakamata su samu duk abinda suke so. Sannan kuma akwai waɗanda suke son nuna su masu wayau ne.
Buhari yace ba zai yi kewar karagar mulki ba saboda tsangwamar da ake masa.
Ina tunanin da wuya zan yi kewa sosai. Ina tunanin cewa ana tsangwama ta.
Da yake magana a wurin, mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo yace shugaba Buhari mutum ne mai kaifi ɗaya wanda yake da kirki matuƙa.
Shugaba Buhari mutum ne mai barkwanci wanda nake tunanin za a dama da shi a fannin nishaɗantarwa idan yayi ritaya. A cewar mataimakin shugaban ƙasar
Ministocin Shugaba Buhari 2 Sun Samu Sarautar Hausa a Daura
Sarkin Daura, Mai Martaba Umar Farouq Bashar ya yiwa ministocin shugaba Buhari naɗin sarauta a masarautar sa ta Daura. Sarkin dai yayi naɗin sarautar ne ga ministoci biyu na gwamnatin Buhari.
Bikin naɗin sarautar ya gudana ne a ranar Alhamis, 22 Ga watan Disamban 2022 a masarautar dake birnin Daura cikin jihar Katsina.
Ministan wasanni da takwaran sa ƙaramin ministan man fetur sune aka gwangwaje da sarautar.
Asali: Legit.ng