Gwamnatin Buhari Ta Kashe N5bn Wajen Gyaran Ofisoshin ’Yan Sanda da Bariki a Cikin Shekaru 3

Gwamnatin Buhari Ta Kashe N5bn Wajen Gyaran Ofisoshin ’Yan Sanda da Bariki a Cikin Shekaru 3

  • Gwamnatin Najeriya ta bayyana adadin kudaden da ta kashe wajen ingantawa da habaka ayyukan hukumar 'yan sanda
  • Gwamnatin Buhari ta ce, a cikin shekaru kasa da uku, ta kashe sama da Naira biliyan wajen gyara da habaka ofisoshin 'yan sanda
  • Gwamnatin Buhari ta sha bayyana aniyarta na samar da wadatattun kayan aiki ga hukumar 'yan sanda

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ta bayyana cewa, ta kashe akalla Naira biliyan 5 wajen gyara ofisoshin ‘yan sanda da barikin soja a fadin kasar nan tsakanin 2019 zuwa 2022.

Hakazalika, gwamnatin ta ce ta yi ingantayya ga wasu wuraren horon jami’ai da cibiyoyi, ciki har da gyaran gine-gine da samar da asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya.

Gwamnatin Buhari ta kashe N5bn wajen gyara ofisoshin 'yan sanda
Gwamnatin Buhari Ta Kashe N5bn Wajen Gyaran Ofisoshin ’Yan Sanda da Bariki a Cikin Shekaru 3 | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Wannan batu na fitowa ne daga bakin ministan harkokin ‘yan sanda na Najeriya, Maigari Dingyadi yayin da yake tsokaci game da tasirin gwamnatin Buhari daga 2015 zuwa 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Najeriya Ta Bada Hutun Kirsimeti Da Sabon Shekara

Wuraren da hukumar ta gyara

Dingyadi ya kuma bayyana wasu daga cikin barikin soja da aka gyara da suka hada da na Kebbi, Edo, Borno, Yobe, Gombe, Bauchi, Plateau, Abia, Bayelsa, Nasarawa, Niger, Sokoto, Ogun, Lagos da babban birnin tarayya Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma shaidawa manema labarai cewa, gwamnati ta kashe wa rundunar ‘yan sandan Abuja N1.3bn, ta gyara makarantar ‘yan sanda dake Enugu a kan kudi N1.2bn da kuma kafa sabon sashen kiyaye manyan laifukan yanar gizo.

Ta ina aka samu kudaden wadannan ayyukan?

Ya bayyana cewa, ayyukan da aka yi an yi su ne ta hanyar asusun tallafin hukumar ‘yan sanda ta Najeriya, This Day ta ruwaito.

Hakazalika, ya bayyana nasarori da hukumar ta samu wajen habaka manhajar horo ga cibiyoyin horo da karantarwa na hukumar.

A bangare gudan, gwamnatin shugaba Buhari ta sha bayyana manufar inganta ayyukan hukumar ‘yan sanda ta hanyar ba jami’ai horo mai inganci.

Kara karanta wannan

Daga karshe, DSS sun kamo wadanda ke kitsa kone ofisoshin INEC a wata jiha

An gurfanar da 'yan APC da PDP 14 a Borno bisa aikata wani babban laifi

A wani labarin kumwa, rundunar 'yan sandan jihar Borno ta ce ta gurfanar da wasu mutum 14 da ake kyautata zaton suna son tada zaune tsaye a jihar.

Wadanda aka gurfanar din sun hada da mambobin APC 12 da kuma na PDP biyu yayin da aka samu hargitsi a wurin kamfen.

Wannan ya faru ne jim kadan bayan da aka farmaki tawagar dan takarar shugaban kasa na PDP, Aiku Abubakar a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.