Bayan Wata Bakwai da Saurayi ya Tasheta a Twitter, Yayi Wuff da Kyakyawar Budurwa

Bayan Wata Bakwai da Saurayi ya Tasheta a Twitter, Yayi Wuff da Kyakyawar Budurwa

  • Wani matashi 'dan Najeriya yayi wuff da wata budurwa da ya hadu da ita a dandalin Twitter, watanni bakwai da suka wuce bayan haduwarsu da juna
  • Amaryar mutumin mai suna Fatima Faguju ta wallafa hotunan bikin aurensu a shafinta na Twitter a ranar Alhamis, 22 ga watan Disamba
  • Ta kara da wallafa hirar tasu mai dadi ta farko mai dadi, wacce ta fara da sallama da barka da sallah tare da hotunan bikinsu

Igiyar aure ta kullu tsakanin wani matashi 'dan Najeriya da wata Budurwa da suka hadu a Twitter. Kyakyawar budurwar mai suna Fatima Faguji ta wallafa hotunan bikinsu a ranar 22 ga watan Disamba.

Amarya da Ango
Bayan Wata Bakwai da Saurayi ya Tasheta a Twitter, Yayi Wuff da Kyakyawar Budurwa. Hoto daga Twitter/@fatimafaguji
Asali: Twitter

Amaryar ta wallafa hotunan bikinsu da hirarsu ta farko a Twitter

Hirar takaitacciya ce, inda yayi mata barka da salla sannan Yahaya (Angon) ya shedawa Fatima irin kyan da take da shi.

Kara karanta wannan

Da Kaina na Ja Masa: Budurwa Ta Tafkawa Tsohon Saurayinta Asiri da Jininta Kan Kin Karbar Cikin da Yayi Mata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haduwarsu ta dandalin sada zumuntar ta haifar da kyakyawan aure wanda dukkansu suke murna da shi.

Fatima ta rubuta a shafinta na Twitter:

"A makon da ya gabata mun yi wani abu, sai dai na manta ban baku labari ba...yay. Nayi aure ga masoyina wanda muka hadu watanni bakwai a Twitter. Allah mai girma Alhamdulillah."

Yayin martani game da wallafar Twitter, Yahaya mijinta ya rubuta:

”Barakallah MashaAllah ! Ina godiya ga Allah bisa wannan kyautar da wasu masu biyowa, ina rokon Allah Ta'ala yasa mana albarka a wannan auren. Ina kaunarki matuka sama da kalmomin baki matata."

Martanin da aka yi musu 'yan dandalin Twitter

@its_ahmard ya ce:

"Ka tabbatar Eidi ne. Ka binciko garin da take. Fada mata iyayenta sun yi sa‘ar samun 'diya kyakyawa kamarta."

@iamremraj ya ce:

Kara karanta wannan

Rudani: Tinubu ya hada kura, bidiyo ya nuna lokacin da yake ba wani dattijo tsabar kudi

"Ina taya ku murna mutanen kwarai. Ubangiji yayi albarka ga gidanku."

@Musakallah yayi tsokaci:

"Ina taya ku murna, Fatima. Nayi matukar farin ciki, Ubangiji ya sanya albarka a rayuwarku ta aure. ameen"

@abdullahhi_ ya ce:

”Gaba daya wannan abun ya faru ne a watanni bakwai fa. Ubangiji ina rokonka ina so in kawo karshen wannan soyayyar a wannan makon."

Yarinya ta mahaifiyarta cizo bayan tayi wa mahaifint ihu

A wani labari na daban, wata karamar yarinya ta kawai mahaifiyarta cizo sakamakon ihun da ta ga tayi wa mahaifinta.

A bidiyon da ya bayyana, an ga karamar yarinyar tayi yunkurin gartsawa mahaifiyarta cizo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

iiq_pixel