Hukumar DSS Ta Kama Wasu da Ke Shirya Kai Hare-Haren Kan Ofisoshin INEC a Jihar Imo
- Hukumar DSS ta bayyana kame wasu da ake zargin su suke kone ofisoshin hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Imo
- Wannan lamarin ya kai ga kwato makamai da kayayyakin aikata laifi da yawa daga hannun tsagerun
- Hukumar INEC na ci gaba da fuskantar matsalolin hare-haren 'yan ta'adda a yankin Kudancin Najeriya
Jihar Imo - Daraktan hukumar tsaro ta farin kasa (DSS) a jihar Imo, Wilcox Idaminabo ya bayyana cewa, DSS ta kame wasu 'yan bindigan da ake zargin sun kitsa kai hari kan hedkwatar hukuma zabe ta INEC a jihar.
An kama 'yan bindigan ne a lokacin da suke kokarin tserewa bayan da suka yi kokarin farmakar hedkwatar, inji rahoton Leadership.
Daraktan ya bayyana cewa, DSS ta yi babban aiki wajen kame 'yan bindigan da ke kitsa ayyukan ta'addanci a jihar, tare da cewa, hukumar za ta ci gaba da aikin tabbatar da tsaro a jihar.
Ya bayyana nasarar da hukumarsa ta samu ne a birnin Owerri ta jihar yayin zantawa da masu ruwa da tsaki tare da kwamishinan hukumar zabe, Farfesa Sylvia Uchenna Agu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban na DSS ya kuma shaida cewa, wani samamen jami'an hukumar ya kai ga kame wani Engr. Mike Ahiz da ake zargin shugaban wasu 'yan daba ne a yankin Orsu.
A cewarsa:
"Muna ci gaba da kakkabe sansanoninsu da maboyarsu a Orsu, Njaba, Orlu da Okigwe, kuma a kokarinmu na aiki a Njaba mun kame wani Ejima wanda ke barazanar kone jihar gaba daya.
"Ina farin cikin sanar da jiya da dare (Talata) muka kame shi yanzu hana yana hannunmu."
An fatattaki 'yan ta'addan, an kwato kayayyakin aikata laifi
Ya kara da cewa, a aikin da suka yi a sansanin 'yan ta 'addan a Orsu, ya kai ga tashin 'yan ta'addan suka kaura zuwa yankin Aku/Ihube a kusa da babbar hanyar Okigwe, inda suka ci gaba da kai hare-hare.
Hakazalika, ya ce jami'an sun kuma kwato kayayyakin aikata laifuka da dama, Punch ta ruwaito.
Idaminabo yace:
“Mun kuma kwato layu, makamai da guraye daga wurinsa."
Daga karshe ya shawarci al'ummar jihar Imo da su ci gaba da ba hukumar hadin kai wajen tabbatar tsaro da zaman lafiya.
Baya ga masu kone ofisoshin gwamnati, ana ci gaba da kame 'yan bindigan da ke addabar jama'a a kasar nan.
Asali: Legit.ng