Ba Abinda Zamuce Game Da Batun Emefele Maganar Tana Kotu

Ba Abinda Zamuce Game Da Batun Emefele Maganar Tana Kotu

  • A farkon satin nan da muke ciki ne wata shari'a ta bayyana, inda aka jiyo hukumar DSS, na neman kotu ta bata damar kama gwamnan babban banki CBN
  • Hukumar DSS, ta zargi Godwin Emefele da daurewa ta'addanci gindi, ta hanyar daukar nauyin aiyukansa a Nigeria.
  • Babban alkalin Kotun mai shari'a Tsoho ya ki bada umarnin, yana mai tabbatar da wanda ake son kamawa din an gaza kawo hujjar da zata sa a kamashi

Abuja: Fadar shugaban kasa ta magantu a ranar larabar nan kan batutuwan da suka maimaye gwamnan babban banki kasa CBN, Godwin Emefele.

Fadar tace ba abinda zata ce illa ta jira taji abinda kotu zatayi.

"Bazamu ce komai akan wannan batu ba sabida batun yana kotu, mun gode da tuntubar mu da kukayi,"

Kara karanta wannan

Da alamun Gudaji Kazaure na da gaskiya, Kotu ta hana DSS kama Gwamnan CBN

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa hukumar tsaron farin kaya ta DSS, sun nemi da kotu ta basu damar kama gwamnan sabida suna zarginsa da sa hannu wajen daukar nauyin aiyukan ta'addannci.

CBN Govnor
Ba Abinda Zamuce Game Da Batun Emefele Maganar Tana Kotu Hoto: The Guardian
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da cewa alkalin babbar kotun da ke zamanta a Abuja, mai shari'a John Tsoho ya hana tare da kin bawa hukumar umarnin, yana mai cewa abinda hukumar din ta ke son aikata ya sabawa doka, sannan hukumar na son amfani da kotun ne dan aikata wani laifi.

Wanne Hukunci Ya Yanke Lokacin Shari'ar

Lokacin da yake yanke hukunci tsakann hukumar tsaron farin kaya ta DSS, da kuma Gwamnann Babban bankin kasa, mai Shari'a Tsoho yace wanda suke kara sunkasa kawo wasu kwararen hujuji da kuma gamsassun bayanai da zasu sa kotu ta amince musu da wannan bukata

Kara karanta wannan

Zabe ya karaso, Hukumar INEC ta Jero Manyan Abubuwa 2 da take Tsoro a 2023

Alkalin ya ci gaba da cewa wannan neman umarnin wani batun ne mai zaman kansa, wanda kuma ya kasa kare kansa kan batun kama wanda hukumar take son ta kama, sabida haka dole a bawa wanda ake so a kama 'yancin da doka ta bashi na kar a kama shi.

Sannan mu mun cika da wani rudani, sabida takardar da hukumar ta rubuto mana bata nuna Godwin Emefele a matsayin gwamnan banki ba, kawai tace Godwin Emefele, to wanne? gwamnan banki ko kuma wani ne daban inji alkali

"Dole in kuna bukatar irin wannan umarnin sai kun kawo hujja mai kyau kan yadda kotu zata gamsu ta baku umarnin

Kamar yadda wannan batun yake a kotu, haka ma fadar gwamnatin tarayya ta hannun mai magana da yawun shugaban kasa Mallam Garba Shehu tace wannan batun yana kotu, basu isa suce komai akai ba

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida