Bayan Kowa Ya Yi Ankon N150k, an Nemi Amarya a Ranar Aurenta an Rasa, Jama’a Sun Girgiza

Bayan Kowa Ya Yi Ankon N150k, an Nemi Amarya a Ranar Aurenta an Rasa, Jama’a Sun Girgiza

  • Jama’a a kafar sada zumunta sun yi martani kan wani bidiyon gidan biki da kowa ya yi ankon N150k
  • A bidiyon da ya yadu a kafar sada zumunta, an ce an nemi amarya an rasa, bakin da suka yi anko kowa ya tsaya carko-carko
  • Wasu mutane a TikTok sun sha dariya, wasu kuma suna bayyana rashin daidaito a labarin da aka bayar

A ranar da ya kamata ta zama abin alfahari, farin ciki da annashuwa, an nemi wata amarya a Najeriya a rasa a ranar bikinta.

A cewar wani shaidan gani da ido da ya yada bidiyon yadda lamari ya faru TikTok, mutane sun kashe N150k a matsayin kudin anko.

A gajeren bidiyon, an ga maza da mata sun yi carko-carko a gidan bikin yayin da suke jiran isowar wata.

Kara karanta wannan

Rudani: Tinubu ya hada kura, bidiyo ya nuna lokacin da yake ba wani dattijo tsabar kudi

Wani mutum da ake kyautata zaton shine angon an ganshi cikinkaya kwat, yayin da yake zagaye da wasu abokansa cikin shudin manyan riguna.

Amarya ta fece, kowa ya yi carko-carko
Bayan Kowa Ya Yi Ankon N150k, an Nemi Amarya a Ranar Aurenta an Rasa, Jama’a Sun Girgiza | Hoto: TikTok/@tobytwerk
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit.ng dai bata tabbatar da batun cewa amaryar ta fece bane, kamar yadda shaidan ya fada har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Bidiyon ya jawo cece-kuce a kafar TikTok, mutane da yawa sun yi martani mai daukar hankali game da wannan amarya.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

Ga kadan daga abin da jama’a ke cewa a kafar TikTok:

Miriam:

"Ina fatan dai kwanon shinkafa ya iso saboda ba wanda zan tura ma sako, kawai a debo min shinkafa, ku ma bar namanku ya huta.”

alexbrenda362:

"Wayyo Allah, na rantse wannan ba zai sake kawo batun aure ba da wata nan gaba.”

mhizz temmhie23:

"Babu wanda yake siyar da anko 150 kuma ma shin kuna da 150k? Kuma ya kamata mutane suke tabbatarwa kafin yin martani a kan komai.”

Kara karanta wannan

Kamar da wasa: Amarua ta ce ba za a daga bikinta ba, ta zo wurin biki da ciwo a kafa

Phresh_bangz:

"Ta yaya aka yi kawayen suka riga ta zuwa, ba kamata ya yi su zo tare ba.”

@demmylahdey:

"Kyakkyawan kari mai tsini kenan.”

Folakemi Adaranijo:

"Amma dai ina kunzo ganin amaryar ne, ku ci abinci kawai, ku yi rawa ku koma gida kawai.”

Agbekeade Tawakalitu:

"Abin da na sani kawai shine ankon nan bai kai 150k ko dai ba kayan bane nake gani a cikin bidiyon.”

Ango ya fasa auren budurwar saboda ta haifi ‘ya’ya kafin su hadu

A wani labarin kuma, wani ango ya fasa auren budurwarsa saboda ya gano tana da ‘ya’ya biyu alhali bai sani ba.

Jama’ar kafar sada zumunta sun yi mamakin wannan lamari, sun yi martani tare da karfafa gwiwar angon.

Ba sabon abu bane a samu ango ko amarya ta fasa aure saboda wani dalilin da ke gindayawa a tsakanin juna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.