Shugaban Makaryata - Lokacin Da Tsohuwar MInistar Kudi Ta Karyata Peter Obi A Bainar Jama'a

Shugaban Makaryata - Lokacin Da Tsohuwar MInistar Kudi Ta Karyata Peter Obi A Bainar Jama'a

  • Mutunci da kimar Peter Obi dai na kila-wa-kala, bayan yadda ake samun wasu faifan bidiyo kan batun da yake yawan fada
  • Kafin nan ana yawan zargin Peter Obi da shaci fadi wajen alkaluma da yake yawan fada ba tare da tabbacin su
  • A wannan bidiyon anga yadda tsohuwar ministan Kudi, Kemi Adeson ke bayyanawa mahalarta wani taro cewa yadda Obin ya fadi wasu kalmomi ba haka suke ba.

Abuja: Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Lp, Peter Obi ya shahara wajen shaci fadi kan kiddiga da fadar kalmomi da ba haka suke ba.

Kafin yanzu, abokan adawar sa na jam'iyyar APC, na yawan sukan tsohon gwamnan jihar Anambra din kan yawan fadan kalmomi da suke na shaci fadi, da molan ka.

Kara karanta wannan

Rudani: Tinubu ya hada kura, bidiyo ya nuna lokacin da yake ba wani dattijo tsabar kudi

A wani bidiyo da Legit.ng ta samu a kafar Twitter, anga yadda Peter Obi din na fadin wasu alkaluma ba dai-dai ba yayin da tsohuwar ministan ke gyara masa.

Abinda tsohuwar ministan ta fadawa peter obi shi ne:

"Ina peter obi ya kamata ku dawo min da shi, ina so zan fada masa wasu kalmomi"

An gani a bidiyon tana yabon gwamnan, amma tace akwai kura-kurai da yawa da ya fada lokacin da yake fadar wasu kididdiga.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tsohuwar ministan tace:

"bana son na ce wasu daga cikin lissafin da Peter din ya fada akwai kuskure, to ya na'iya akwai kuskure a ciki"

Duk da haka dai Peter Obi zai kara da Atiku da Bola, a matsayin babban dan hamayyar su.

Wasu dai na ganin Obin zai samu goyan bayan yawancin matasa ne da ake ganin sune suka fi kowa yawan yin katin zabe.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Okupe Yayi Murabus Daga Matsayin DG na Kamfen din Peter Obi

Da Ina Tinubu Yake Takama Ne?

Shi kuwa dan takarar jam'iyyar APC, Bola Tinubu ana ganin yanad goyan bayan gwamnaonin jihohin arewa ne da kuma wasu a yankin kudu maso yamma.

Abinda jira a gani dai shine yadda za'ai zaben da yake kara karatowa wanda za'ai zaben shugaban kasa a watan fabairun 2023 hade da yan majalissar wakilai da sanatoci.

Yayin da zaben gwamnoni da yan majalissar jiha kuwa za'ayi ne a watan uku wato watan Maris din shekarar dai.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida