Shugaba Buhari Ya Sa Labule da Kakakin Majalisar Wakilai Kan Muhimman Abu 2

Shugaba Buhari Ya Sa Labule da Kakakin Majalisar Wakilai Kan Muhimman Abu 2

  • Shugaban kasa Buhari ya sa labule da kakakin majalisar wakilan tarayya a fadarsa da ke Abuja kan muhimman abubuwa
  • Femi Gbajabiamila yace sun tattauna batutuwan da suka shafi sabon tsarin CBN da kuma babban zaɓe mai zuwa
  • Wannan ganawa ta zo ne a ranar da gwamnan CBN ya sake kauracewa gayyatar mambobin majalisar wakilai

Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi ganawar sirri da kakakin majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, a fadarsa da ke Abuja ranar Talata 20 ga watan Disamba, 2022.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa a taron, shugabannin biyu sun tattauna kan sabon tsarin taƙaita yawon takardun kuɗi wanda ya haddasa cece-kuce a sassan kasar nan.

Shugaba Buhari da kakakin majalisar wakilai.
Shugaba Buhari Ya Sa Labule da Kakakin Majalisar Wakilai Kan Muhimman Abu 2 Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: UGC

Idan baku manta ba a 'yan kwanakin nan, babban bankin Najeriya karkashin jagorancin Godwin Emefiele ya sanar da sabon tsarin wanda ya ƙayyade iyakar kuɗin cirewa.

Kara karanta wannan

Rigimar PDP: "Saura Kiris" Gwamnan Tsagin Wike Ya Faɗi Yuwuwar Su Yi Wa Atiku Aiki a 2023

Bayan tsarin takaita yawon kuɗi a hannu, shugabannin sun kuma tattauna wasu batutuwan da suka shafi babban zaben 2023, inji Femi Gbajabiamila.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Akwai abubuwan da suka taso game da tsarin takaita yawon kuɗi a hannu, batutuwan da suka shafi zaɓe da rikice-rikice dake faruwa nan da can, sune muka maida hankali da wasu muhimman abubuwan."

Wannan taron na zuwa ne a ranar da gwamnan CBN ya sake watsi da gayyatar majalisar wakilan tarayya karo na biyu.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa majalisar wakilai ta gayyaci gwamnan CBN ne domin ya musu karin haske kan sabon tsarin, da kuma takaita cire kuɗi zuwa N20,000 kowace rana.

Meyasa gwamnan CBN bai amsa gayyatar ba?

Gwamnan CBN ya rubuta wasika zuwa ga mambobin majalisar, inda ya faɗa masu ba zai samu zuwa bane saboda ba ya cikin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Aike da Wasika Zuwa Garuruwa Hudu, Sun Faɗi Lokacin Kai Hari

A wani labarin kuma Kotu Taki Amincewa Da Bukatar DSS Na Kama Gwaman Babban Bankin Najeriya

Wani ɗan sanda ya bayyana wa manema labarai takardar da DSS ta roki mai alƙalin Kotu ya yi umarnin kama gwamnan CBN kan wasu dalilai.

An tattaro cewa hukumar yan sandan farin kayan ta nemi kama shi ne kan zargin zamba cikin amince, harkallar wasu kudade da yi wa tattalin arziki rikon sakainar kashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262