'Yan Crypto a Najeriya Sun Nuna Biliyoyin Kudaden da Aka Tura Zuwa Asusun Su Bisa Kuskure

'Yan Crypto a Najeriya Sun Nuna Biliyoyin Kudaden da Aka Tura Zuwa Asusun Su Bisa Kuskure

  • 'Yan Najeriya sun shiga jimami bayan ganin biliyoyin daloli a asusunsu na crypto amma aka debe cikin gaggawa
  • Mutane da yawa sun yada hotunan asusunsu na Coinbase, wata kafar crypto da ta yi kuskuren tura kudi asusun jama'a
  • Kafar Coinbase ta fito ta yi bayanin abin da ya faru, ta ce an samu wani tsaiko ne a fasahar manhajojinta

Da yawna ‘yan crypto a Najeriya sun wayi gari da tarin biliyoyin daloli a asusunsu yayin da wata kafar crypto ta samu matsalar fasaha.

Bayan da Legit.ng ta yada labarin Chinedu MacGordon da ya wayi gari da tarin biliyoyi a asusun crypto dinsa, jama’a da yawa ne suka yi martani da labari mai kama da nasa a kafar Facebook.

Da yawan mutane sun bayyana cewa, sun ga tarin kudi a asusunsa na Coinbase, kuma sun yi kokarin cire kudin, amma hakan ya gagara.

Kara karanta wannan

Gandoki: An Sha Dirama Yayin da Iyali Suka Isa Wajen Biki Sanye Da Anko Wata Guda Kafin Ranar Auren

Yadda 'yan crypto suka yi arzikin rana daya, komai ya sauya
'Yan Crypto a Najeriya Sun Nuna Biliyoyin Kudaden da Aka Tura Zuwa Asusun Su Bisa Kuskure | Hoto: Facebook
Asali: Facebook

Wasu kuwa cewa suka yi biliyoyi kawai suka gani, amma suka bace nan da nan, lamarin da ya sosa ran 'yan crypto da yawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin da ‘yan crypto ke cewa

Larry Ubah:

“Asusu na na crypto ya kusan kama dala biliyan 48 lokacin da aka samu matsalar. Kawai ina kallon kudi ne irin wadannan amma ina jin haushin kaina.

Muhammad Nura Muhammad:

“Ai jiya da dare na fara tunanin za a buga suna na a jerin attajirai na Forbes.”

And Paul G Jnr:

"Abin na sani kawai shine na kafa tarihi, na taba zama biloniya mai daloli na rana daya. Kar ku ce min komai.”

Steve:

"Kudin da bai wuce #2600 ba amma na tashi cikin dare na ga Naira tiriliyan 44. Na ji har na zama tiriloniya a rayuwata.”

Njoku Obinna Godsboy:

Kara karanta wannan

Alhamdulillahi: 'Yan sanda sun kama wasu tsagerun masu garkuwa da mutane

"Lokacin da na ga abin, na kira manaja na nace ya fara canji da siyarwa nan take, har ce masa na yi idan harka ta kankama zai siya masa mota Benz a wannan kirsimetin. Ba zan manta jiya cikin sauri ba.”

An taba samun haka, kuskure ne

Idan baku manta ba, a ranar 14 ga watan Disamban 2021, masu amfani da Coinbase sun taba tashi tare da ganin kudade mara misaltuwa a asusun crypto, rahoton NairaMetrics.

Da yawa a wancan lokacin sun yanke sun zama attajirai, amma kamfanin ya sanar da cewa ya samu tsaiko ne.

A kafar Twitter, Coinbase ta fito ta yi bayanin cewa, wasu daga cikin kwastomominsa sun ga kudi, amma fa hakan kuskure ne.

Don haka kamfanin ya yi karin haske tare da bayyana matakin da yake dauka, lamarin ya dauki hankalin jama’a.

Bayan kaddamar da kudaden Najeriya da aka sauyawa fasali, ana samun tsaikon yawon kudaden bogi, rahoto ya bayyana mafita game da hakan.

Kara karanta wannan

Gwamna ya Umarci a Damke Kukun da Tayi Abincin Liyafar Kirsimati da ya Shirya, Yace Babu Dadi

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.