Buhari: Da Gangan Na Shirya Tafiya Ranar Don Gujewa Shagalin Bazday

Buhari: Da Gangan Na Shirya Tafiya Ranar Don Gujewa Shagalin Bazday

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da yadda ya shirya dawowa Najeriya daga Amurka don gujewa shagalin ranar zagayowar haihuwarsa
  • Cike da annashuwa da jin dadi ya mika godiyarsa ga dukkan wadanda suka aika masa da katika tare da fatan alheri yayin da ya cika shekaru 80 a duniya
  • Wasu ma'aikatansa a safiyar Litinin sun je taya shi murna sannan ya duba katikan da aka kai masa kafin ya umarci a koma bakin aiki

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya bayyana godiyarsa kan katika da fatan alheri da ya samu daga jama'a bayan cikarsa shekaru 80 da haihuwa, jaridar Leadership ta rahoto.

Shugaba Buhari
Buhari: Da Gangan Na Shirya Tafiya Ranar Don Gujewa Shagalin Bazday. Hoto daga Garba Shehu
Asali: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa, sai dai cike da wasa, yace fatan da yayi na samun rana mara hayaniya ya rasa ta daga ma'aikatansa inda ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Kaico: Dan Hisbah ya yi babban laifi, Kotun Kano ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya

"Na saka tafiyata daga Amurka da gangan a ranar don gujewa shagali."

Kamar yadda takardar da mai magana da yawun shugaban kasan, Garba Shehu ya fitar, Farfesa Ibrahim Gambari, Boss Mustapha da wasu kebantattun ma'aikatan shugaban kasan sun tari a gidansa da safe don taya shi murnar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaba Buhari yace ranar zagayowar haihuwarka bata wuce wata irin rana ba da kake ofis.

A wani jawabi a madadin ma'aikatan shugaban kasan, shugaban ma'aikatan ya karanta katin da suka aike masa da sa hannunsu a bayyane kamar haka:

“A madadin dukkan ma'aikatan da ni kaina, muna murnar ranar zagayowar haihuwar shugaba nagari, uban kasa kuma ubanmu.
"Ranka shi dade tauraro ne da a taron shugabannnin Amurka da Afrika wanda shugabannin suka samu halarta.
"Muna alfahari da kai ranka shi dade kuma muna godiya kan damar da ka bamu ta aiki karkashinka da mutuntawa."

Kara karanta wannan

Bukatu 6 da Muka Gabatarwa Buhari Sa'ilin da Muka Zauna da Shi Inji Aminu Daurawa

Buhari ya zaga dakin inda ya dinga karanta katikan daya bayan daya sannan daga bisani ya umarci kowa ya koma ofishinsa.

"A koma bakin aiki,"

- Yace yayin da ya kama hanyar zuwa inda ofishinsa yace.

Shugaban kasan ya cigaba da taruka da sauran ayyukansa a ofishinsa har zuwa karshen ranar.

Shugaba Buhari ya cika shekaru 80 a duniya

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika shekaru 80 a duniya a ranar Lahadi, 18 ga watan Disamban 2022.

A ranar yana kan hanyarsa ta dawowa gida Najeriya daga kasar Amurka inda ya halarci wani taro amma ma'aikatansa sun shirya masa kek don taya shi murna

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng