Ibrahim Shekarau Sha-Sha-Sha Ne, Allah Ya Tsine Masa: Fani-Kayode
- Musayan yawu ya kaure tsakanin tsohon Ministan Ilimin Najeriya da tsohon Ministan Sufuri
- Dukkansu biyu na kare muradun wadanda suke goyon baya ne a zaben shugaban kasan 2023
- Fani-Kayode ya tsinewa Malam Shekarau kuma ya kira sa da mayaudari kuma maras tunani
Diraktan kafafen ra'ayi da sada zumunta na kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar All Progressives Congress APC, Femi Fani-Kayode ya yi dirar Mikiya kan tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau.
Wannan ya biyo bayan jawabin da Malam Ibrahim Shekarau yayi kan lafiyar dan takarar shugaban kasan jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.
Shekarau ya bayyana cewa Tinubu fa ba isasshen lafiya garesa ba kuma kada a zabesa matsayin shugaban kasa.
Yace:
"Shin karya muka yi da muka ce yana fama da matsanancin rashin lafiya? Ta wani dalili zaku zabeshi matsayin shugaban kasa."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Fani Kayode yayi martani
Femi Fani-Kayode ya yi martani mai zafi kan Shekarau inda ya kira shi da sha-sha-sha kuma ya tsine masa albarka.
A cewar Fani-Kayode, Atiku ne mara lafiya kuma ko zama a Najeriya ba ya yi, kasar Dubai yake zama.
Ya bayyana hakan ne a jawabin da ya fitar a shafinsa na Tuwita.
Yace:
"Kalaman yaudara da rashin hankali daga bakin mayaudari kuma sha-sha-sha."
"Allah sa Aradu ta ya kashe ka. Atiku ne mara lafiya ba Asiwaju ba. Bamu bukatan mata-maza wanda ke zama a Dubai. Mutumin kwarai irin Tinubu muke bukata."
Fani Kayode Ya Gargadi Masu Nufin Tinubu Da Sharri, Ya Ce Babu Wanda Ya Isa Ya Kashe Shi Sai Allah
A wani labarin daban, Diraktan na kafafen ra'ayi da sada zumunta na kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar All Progressives Congress APC, Femi Fani-Kayode, ya ba dai mutum ba sai Allah, babu wanda zai iya kashe Tinubu.
Hakan ya biyo bayan kalaman katobarar da dan takaran shugaban kasan na APC ke yi a tarukan yakin neman zaben da yake halarta.
Wasu suna cewa gwamnonin Arewa na goyon bayan Tinubu ne saboda suna sa ran zai mutu nan ba da dadewa ba kuma mulki ya koma hannun dan Arewacin Najeriya.
Asali: Legit.ng