Hukumar EFCC, Basu Da Hurumin Dokar Bincikar Yadda Jihohi Suke Kashe Kuɗaɗensu
- Hukumar hana ta'annati da dukiyar gwamnati EFCC bata da hurmunin da zata tuhumi ko binciki yadda jihohi ke tafiyar da kudinsu kamar yadda tsohon shugaban NBA ya fada.
- Masana shari'a na ganin EFCC din na wuce gona da iri wajen gudanar da aiyukanta, kamar yadda aka gani lokacin da suka shiga gidan tsohon gwamnan Imo Rochas.
- Dokokin da suka kafa hukumar sun fayyace aiyukan da hukumar zata iya yi, da kuma wanda takwarorinta zasu. .
A wajen tsohon shugaban ƙungiyar baristoci ta ƙasa NBA, Dr Olisa Agbakoba (SAN), yace hukumar EFCC, bata da hurumin bincikar kudin ƙananan hukumomi. Rahotan The Nation
Ya ci gaba da cewa babban kotun kasa ta riga ta fayyace iyaka da kuma bodar da hukumar zata iya shiga kamar yadda yake a sashi na 46 na kafa hukumar, wanda bai kunshi jihohi ba.
Ya yarda cewa hukumar EFCC, tana da rawar da zata taka wajen yakar cin hanci da rashawa, amma yace hukumar tai kaurin suna wajen taka doka da oda.
Agbakoba yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Yanzu kamar wannan abun da ake ta yamididinsa na EFCC din ta kama wasu da zargin satar kudi a jihar Kogi, abin sani na shine ba hurumin EFCC bane, sabida ba inda ake ce EFCC ta binciki ya kogi take kashe kudinta."
"kwananma sai da babbar kotun kasa tace ba wai hutumin EFCC bane shiga ko wanne batun harkallar kudi ba, dole ne ta bi doka da oda a duk abinda zatai."
Yya shawarci hukumar kan ta maida hankali wajen ganin ta bi dokar da ta kafa ta, ya a mai cewa:
"Idan kuna son ku ƙara samun dama ko buɗi a aikinku zaku iya zuwa zauren majalissar ƙasa ko kai koken ku sai su ƙara muku.
Ya Kamata A Samu Hukumar Kula Da Kadarorin Gwmnati.
A wani labarin kuma, yayin da Agbakoba yake amsa tambayoyin manema labarai, yace ya kamata ace anyi hukumar kula da kayan da aka kwace daga hannun wanda aka kwace din.
Yace rashin yin hakan kan sa hukumar yin abinda ta ga dama da kayayyakin ba tare da sanin mai tai da su ba ko wani abu makamancin haka.
Asali: Legit.ng