Mota Guda Muka Cika: Yan Biki Sun Koka Bayan Sun Isa Wajen Taro Suka Ga Wayam Ba Kowa

Mota Guda Muka Cika: Yan Biki Sun Koka Bayan Sun Isa Wajen Taro Suka Ga Wayam Ba Kowa

  • Wata kyakkyawar budurwa da danginta sun yi tafiya kwanan nan don halartan bikin aure amma suka kunshi bakin ciki bayan sun isa wajen
  • Budurwar ta ce basu san ainahin ranar bikin ba har sai da suka isa wajen taron cike da bas daya
  • A cewar Big Baby P a Twitter, bayan sun isa wajen sai aka sanar dasu cewa sai a watan gobe ne za a yi bikin

Wata mai amfani da sunan Big Baby P a Twitter ta bayyana yadda ta kunshi takaici bayan ta yi tafiya tare da ahlinta gaba daya don halartan bikin aure.

Big Baby P ta tuna cewa ahlin nata sun saka kayan anko sannan suka dafa abinci mai yawan gaske har da gayyatan abokai zuwa wajen bikin.

Masu anko
Mota Guda Muka Cika: Yan Biki Sun Koka Bayan Sun Isa Wajen Taro Suka Ga Wayam Ba Kowa Hoto: @Marco Longari
Asali: Getty Images

A ranar da suka yi zaton za a yi bikin, sai suka yi hayar motar bas cike sannan suka tashi daga Lagas zuwa jihar Osun.

Kara karanta wannan

Ta bare: Saura kiris biki ango ya gano budurwarsa na da 'ya'ya 2, ya dauki tsattsauran mataki

Abun takaici, da isarsu wajen bikin, sai aka fada masu cewa ai a wata mai kamawa za yi auren.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ni da ahlina gaba daya mun taba saka anko, muka dafa abinci da yawa sannan muka yi tattaki daga Lagas zuw Osub don halartan bikin da sai a wata mai kamawa za a yi. Har da gayya muka yi, sun bi mu cike da bas daya" Big Baby P ta bayyana.

Jama'a sun yi martani

4ever logic ta ce:

"Na zata jarrabawata karfe 3:00 na rana ne, ban sani ba ashe karfe 8:00 na safe ne kuma ina nan a gida na tasa takardu gaba ina ta karatu."

Ula Mary ta rubuta:

"Haka na yi na siya tikitin taron da za a yi a ranar 10 ga wata na zata 11 ga wata be taron, a wannan ranar ina gida zaune bana komai kadaici ya ishe ni, na ga tikitkn amma ban duba ranar ba sai waahegari naga 10 ga wata. Haka tikitin nan ya tafi a banza."

Kara karanta wannan

Maa Ta Nadi Bidiyon Mijinta Yana Shan Wankin Kayanta, An Yi Cece-kuce

Folake ta tuna:

"Ni da mijina mun je bikin mutuwa mako daya kafin ranar taron a coci. Mun je wajen sai muka tarar ana wani bikin aure. Lokacin ne muka sake duba katin gayyatan. Mijina ne ya je wajen taron shi kadai a ainahin ranar bikin.

Lulu Yoruba ta yi martani:

"Hakan ya faru da wasu iyali mako daya kafin auren. Gaba daya iyakin sun je coci, a cocin ne suka gane cewa makon gobe ne. Sun kuma zo bikin."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng