'Yan Bindiga Sun Aike da Wasika Zuwa Garruruwa Hudu a Jihar Ogun

'Yan Bindiga Sun Aike da Wasika Zuwa Garruruwa Hudu a Jihar Ogun

  • Mazauna wasu kauyuka hudu a ƙaramar hukumar Yewa ta arewa a jihar Ogun sun shiga tashin hankali mai tsanani
  • Wasu da ake zargin Fulani makiyaya ne sun rubuta wasika ga kauyukan sun fada masu shirinsu na kai farmaki
  • Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da lamarin kuma tace ba zata yi kasa a guiwa ba wajen binciko masu hannu

Ogun - Mazauna garuruwan Asa, Agbon, Ibeku da kuma Oja-Odan, a ƙaramar hukumar Yewa ta arewa, jihar Ogun sun shiga tsananin tashin hankali biyo bayan wasiƙar da mahara suka aiko masu.

Rahotanni sun nuna cewa maharan waɗanda ake zargin Fulani makiyaya ne sun aiko wa mazauna ƙauyukan sako, suna ankarar da su shirin su na farmakin ɗaukar fansa.

Mahara a Ogun.
'Yan Bindiga Sun Aike da Wasika Zuwa Garruruwa Hudu a Jihar Ogun Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

Wasikar wacce wakilin jaridar Daily Trust ya gani, an manna ta a Bango na wurare masu muhimmanci a garuruwan da lamarin ya shafa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Bankawa Babbar Kotun Jiha Wuta, Sun Tafka Ɓarna

Yan bindigan sun shaida wa shugabannin yankunan cewa su tsammaci ziyarar ba zata a tsakanin watannin Disamba da Janairu masu zuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasikar ta ce:

"Ku ba mu hankalinku, ku saurara; zuwa ga ƙauyukan Asa, Agbon, lbeku, Oja-odan da sauran kewayensu, shin kuna ganin zaku kori mutanen mu daga gonakin da suka siya a Najeriya?"
"Kun kashe mutanen mu, kun kashe dabbobinsu, kun kwace dukkanin kadarorinsu kuma kuna tunanin kun ci bulus, lokaci ya yi da zamu zo ɗaukar fansa."
"Shugabannin baki ɗaya garuruwan da muka ambata a sama su shirya wa yaƙi tsakanin watannin Disamba da Janairu. Zamu zo kwace kadarorin iyayenmu da kuka gaje."

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya yabbatar da batun, yace ya ga kwafin wasikar.

Oyeyemi ya kore duk wata fargaba kana ya tabbatarwa kauyukan da lamarin ya shafa cewa hukumar 'yan sanda ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen zakulo duk masu hannu.

Kara karanta wannan

Wasu Jiga-Jigan Kwamandojin Boko Haram Sun Mika Wuya A JIhar Barno

"Mun ga wasika daga mutanen da babu tabbacin akwai su, mun yi imani ƙungiyar ba ta inganta ba, amma ba zamu rintsa ba saboda ba'a raina abu komai ƙanƙantarsa."

"Ba mu watsar da batun ba, muna kan aiki don zakulo duk masu hannu a lamarin," inji shi.

A wani labarin kuma Wasu Miyagun 'Yan Bindiga Sun Harbe Daraktan Kwamitin Kamfen Atiku A jihar Ribas

Wasu mutane ɗauke da bindigu da ake zaton yan daban siyasa ne sun harbi Daraktan haɗa kan matasa da PDP-PCC a jihar Ribas, Rhino Owhorkire.

Rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka yana kwance a Asibiti, maharan sun lalata bakinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262