Yanzu-Yanzu: 'Yan Darikar Tijjaniya A Nigeria Sun Marawa Bola Ahmed Tinubu Baya

Yanzu-Yanzu: 'Yan Darikar Tijjaniya A Nigeria Sun Marawa Bola Ahmed Tinubu Baya

  • Shugabbanin darika a jihar Niger sun yabawa gudunmawa da Bola yake bawa addini da darikar a Nigeria.
  • Shugabbanin sun yabi Bola tare da yi masa addu'a a taron zikirin da aka shirya hadi da maulidi a jihar Niger.
  • Duk shekera dai darikar na shirya irin wannan taron ko dan yin mauli ko kuma hadi da zikiran tare da yiwa kasa addu'ar zaman lafiya.

Niger: 'Yan darikar Tijjaniya a Nigeria sun yiwa 'dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu addu'ar samun nasara.

A wani taron zikirin kasa da maulidi da darikar ta shirya a garin Minna na jihar Neja, ta tabbatarwa da Tinubu matsayin uban darikar a Nigeria.

A wata sanarwa da sakataran yada labaran gwamna jihar Niger ya fitar kuma jaridar The Cable ta samu yace wanan zikirin wani bangare na maulidin da darikar Tijjaniya mai suna Ansarul Deeni Attijaniya ta shirya.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Samu Gagarumin Tagomashi, Dubban Mutane Sun Sauya Sheka A Jihar Sokoto

Darika
Yanzu-Yanzu: 'Yan Darikar Tijjaniya A Nigeria Sun Marawa Bola Ahmed Tinubu Baya Hoto: The Cable
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Inyass yace dan takarar jam'iyyar APC yardajjen mutum ne a bangarori da dama da suka hada da gina 'dan adam, bunkasa abubuwan more rayuwa, sannan zai ci gaba da yin haka in aka zabeshi a matsayin shugaban kasa.

Sannan Shehin darikar ya ya roki al'ummar musulmi su ci gaba da addu'a dan ganin zaman lafiyar Nigeria.

A yayin taron zikirin akwai gwamnan jihar Niger, Kano, da karamin ministan harkokin kasar waje, da srakunan gargajiya da kuma tsohon kakakin majalisar wakilai Dimeji Bonkole.

Darikar Taijjaniya Tayi Sabon Halifa

An nada tsohon sarkin kano (na sha hudu) wato Mallam Muhammadu Sunusi Lamido II a matsayin sabon muqaddamin darikar tijjaniya a Nigeria.

Nadin nasa ya biyo bayan rasuwan babban muqaddiminta a Nigeria wato Sheik Isayaka Rabi'u Kano. Za'a iya cewa mukamin dai ya sake komawa jihar kano domin shima tsohon muqaddimin dan jihar kano ne.

Darikar tijjaniya dai suna bin tafarkin shehu Tijjhaniya wanda suke nasabtashi da janibin fiyayyen halitta a matsayin jika ko kuma tattaba kunnensa.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida