Makasan Haya Sun Farmaki ‘Dan Takarar Majalisa, Sun Halaka a Imo

Makasan Haya Sun Farmaki ‘Dan Takarar Majalisa, Sun Halaka a Imo

  • Miyagun ‘yan bindiga da ake kyautata zaton makasan haya ne a ranar Juma’a sun kutsa gidan Chritopher Elehu inda suka halaka shi tare da kone kadarorinsa
  • Har kafin rasuwarsa, Elehu shi ne ‘dan takarar kujerar majalisar jiha na karamar hukumar Onuimo a jihar Imo karkashin jam’iyyar LP
  • Wani ganau da ya bukaci a boye sunansa ya sanar da cewa maksan sun kwashi awa biyu sun harbi a gidan Elehu kafin su zagaya gidajensu wasu ‘yan siyasan amma basu tarar da su ba

Imo - Wasu ‘yan bindiga da ake zargin makasan haya ne a ranar Juma’a sun halaka ‘dan takarar majalisar jiha na karamar Onuimo a jihar Imo, Christopher Elehu.

Majalisar jihar Imo
Makasan Haya Sun Farmaki ‘Dan Takarar Majalisa, Sun Halaka a Imo. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Baya da halaka shi, ‘yan bindigan sun bankawa gidansa wuta inda suka kone kadarorinsa kamarsu babur.

Kara karanta wannan

Katsina: ‘Yan Sanda Sun Ragargaji ‘Yan Bindiga, Sun Kama 2 tare da Ceto Mutum 5 da Suka Sace

Jaridar Punch ta tattaro cewa, wadanda ake zargin sun kai farmaki a sa’o’in farko na ranar Juma’a inda suka dinga harbi sama da awa biyu.

An tattaro cewa, ‘yan bindigan wadanda suka rikice sun ziyarci gidajen ‘yan siyasa a yankin amma basu same su ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ganau yayi bayani

Wata majiya wacce ta bukaci a boye sunanta tace:

“Sun halaka Christopher Elehu wanda aka fi sani da Wasco. Har zuwa rasuwarsa, shi ne ‘dan takarar majalisar jiha na karamar hukumar Onuimo. Sun kutsa gidansa yayin da kowa yayi bacci kuma sun yi harbi tsawon awa biyu.
“Sun halaka mutumin tare da kone gidan. Sun barnata kadarorinsa. Gawarsa na kwance a kasa tare da yanka adda yayin da mazauna kauyen suka taru da safiya.”

Kisan ‘dan siyasan na zuwa ne kwanaki goma bayan da mutuwar ‘dan takarar LP a karamar hukumar Okigwe, Chukwunonye Iruono.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Damke Bogi Kan Zargin Damfara da Mallakar Dalolin Bogi

Iruono wanda zai yi jagorancin ralin kamfen din LP a jihar, ya yanke jiki ya fadi. An gaggauta mika shi Cibiyar Magani ta Tarayya dake Owerri inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Har yanzu ‘yan sandan jihar basu fitar da takarda kan kisan ba.

An yi yunkurin halaka ‘dan siyasa a Niger

A wani labari na daban, wasu ‘yan bindiga sun kutsa gidan ‘dan majalisar tarayya a jihar Neja.

Sai dai cike da rashin sa’a aiwatar da kudirin da ya kai su, na kama su dumu-dumu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng