Bankunan Najeriya Na Fama da Karancin Sabbin Kudade a Najeriya, Bankuna Da ’Yan Kasa Sun Koka
- Sabbin kudaden da gwamnatin Najeriya ta kaddamar makwannin baya tuni suka fara yawo a hukumance a ranar Alhamis 15 ga watan Disamba
- Kwastomomi da yawa a bankunan Najeriya sun bayyana damuwar rashin samun sabbin kudaden a bankunan kasar nan
- Bankunan Najeriya sun koka da cewa, basu samu adadi isasshe na sabbin kudaden daga Babban Bankin Kasa ba (CBN)
A ranar Alhamis 15 ga watan Disamba ne a hukumance aka fara kashe sabbin kudaden da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da sake wa fasali a watan jiya.
‘Yan Najeriya sun yi tururuwa zuwa banki, amma suka samu matsalar rashin samun adadin da suke bukata na sabbin kudaden saboda bankunan da kansu basu sami kudaden da yawa ba.
‘Yan Najeriya sun koka, sun kuma yi martani mai zafi game da rashin samun sabbin kudaden a lokacin da suka nema a bankunan kasar nan.
A nasu bangaren, bankuna a Najeriya sun yi bayani, sun ce basu samu adadin kudaden masu yawa bane daga CBN.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Batun sauya fasalin Naira
Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya ambata a ranar 26 ga watan Oktoba cewa, CBN zai sake fasalin Naira; N200, N500 da N1,000, inda yace tsoffin wadannan kudade kuwa za su daina amfani a watan Janairun badi.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, gwamnan na CBN ya ce, bankin zai yi aiki tukuru wajen tabbatar da rage yawan kudade a hannun jama’a domin magance matsalolin hauhawar farashi, rashin tsaro da yaduwar kudin bogi.
Kwastomomi sun fara kokawa game da rashin sabbin kudade a banki
A jihar Legas, wasu kwastomomi sun ziyarci bankuna da dama, sun kuma bayyana kokensu game da rashin sabbin kudin a kanta.
Da yawan bakunan sukan ce ko dai babu kudaden a kasa, ko kuma sun riga sun rabarwa jama’a.
Wasu bankunan kuwa, sun ce basu samu damar karbar sabbin kudaden daga CBN ba kwata-kwata.
Hakazalika, injunan cire kudi na ATM na ci gaba da bayar tsoffin kudade kamar dai yadda aka saba a baya.
Babu sabbin kudade a wasu bankunan Gombe
Da sanyin safiyar ranar Juma’a, wakilin Legit.ng Hausa a jihar Gombe ya ziyarci daya daga cikin bakunan da ke Commercial Area a jihar, inda ya gwada cire kudi, tabbas tsoffin takardun Naira bankunan ke bayarwa.
Hakazalika, masu sana’ar cire kudi ta POS suna ci gaba da ba da tsoffin kudade ne tare da bayyana cewa, basu samu damar ganin alamar sabbin Naira ba.
A wani bangaren kuma, ya ziyarci wani bankin kasuwanci, nan ma bai samu sabbin kudaden da aka kaddamar ba.
Ma'ikacin banki ya ce bai ga lamar sabbin kudade a bankinsu ba, don haka basu ba wani kwastoma ba.
Wani kwastoman da yazo cire kudi, Muhammad Sa’idu ya shaida cewa:
“Ban san ko a wasu bankuna ba, amma anan dai kam babu alamar sabbin kudi. Ina da aboki mai aiki a nan, ya ce ba a kawo musu sabbin kudi ba.
“Watakila ko Abuja da Legas, tunda a irin can ne komai ke fara tabbata kafin jihohinmu Arewa maso Gabas.”
A wani bankin kuma,Yahya Isa Khalifa cewa ya yi:
“A hoto muke gani, ni dama samun sabbin kudin nan bai dame ni ba. Na saba da amfani da waya ta. Kuma mutane mun cika gaggawa, kwana nawa ne za mu samu sabbin kudin har sai mun gaji?”
Wata mata kuwa, ta koyawa duniya yadda ake ajiyar kudi cikin sauki ba tare da wata matsala ba.
Asali: Legit.ng