Abdussamad Bua na Hamshakin Mai Arziki na 4 a Afrika, Dangote na ta Tafka Asara
- Abdulsamad Rabiu ya shillara cikin jerin wadanda suka fi kowa kudi a Afirka yayin da arzkin sauran yayi kasa
- Forbes ta ruwaito yadda a halin yanzu Abdulsamad ya zama mutum na hudu da yafi kowa arzki a Afirka, mataki daya sama da yadda ya fara a 2022
- Hakan ya faru ne da Dangote da sauran biloniyoyi sukayi asarar sama da N3 triliyan a watanni uku da suka shude
Abdulsamad Rabiu, shugaban kamfani siminti na BUA ya haura zuwa mataki na hudu a jerin sunayen masu kudin Afirka wanda a yanzu ya kere biloniyan nan da Misira, Nassef Sawiris.
Kamar yadda Forbes ta ruwaito, Rabiu ya hada sama da $1.1 biliyan a shekarar 2022, wanda a yanzu yake da jimillar arzikin mai kimar $8.1 biliyan, samar da $7 biliyan yayin da shekarar ta fara.
Haka zalika, kafar dake Amurka ta ruwaito yadda Rabiu ya zama tilo cikin jerin biloniyoyin Afirka 10 da ya samu kumbatsar dukiyarsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tumbatsar arizikinsa na da nasaba da irin namijin kokarin da kadarorin kasuwancin sa suka yi a Najeriya da wadanda suka hada; kamfanin siminti, matatar sukari da kasuwancin gidaje.
Wannan haurawar da yayi da kamfanonin suka samu a kasuwanci ne ya karfafa matsayinsa a Najeriya a matsayin mutum na biyu da yafi kowa kudi a kasar, gami da rufe tazarar dake tsakaninsa da mutumin da yafi kowa arziki a Afirka, Aliko Dangote.
Kimar arzikinsu a watan Janairu 2022
1. Aliko Dangote - $13.9 biliyan.
2. Johann Rupert da iyalansa - $11 biliyan.
3. Nicky Oppenheimer da iyalansa - $8.7 biliyan.
4. Nassef Sawiris - $8.6 biliyan.
5. Abdulsamad Rabiu - $7 biliyan.
6. Mike Adenuga - $6.7 biliyan.
7. Issad Rebrab da iyalansa - $5.1 biliyan.
8. Naguib Sawiris - $3.4 biliyan.
9. Patrice Motsepe - $3.1 biliyan.
10. Koos Bekker - $2.7 biliyan.
Kimar arzikinsu a Disamba, 2022 :
1.Aliko Dangote - $12.9 biliyan.
2.Johann Rupert da iyalansa - $ 9.6 biliyan.
3.Nicky Oppenheimer da iyalansa - $8.6 biliyan.
4.Abdulsamad Rabiu - $8.1 biliyan.
5.Nassef Sawiris - $7 biliyan.
6.Mike Adenuga - $5.8 biliyan.
7.Issad Rebrab da iyalansa - $ 5.1biliyan.
8.Naguib Sawiris - $3.4 biliyan.
9. Patrice Motsepe - $2.7 biliyan.
10.Koos Bekker - $2.5 biliyan.
Dangote ya samu karuwar N2.49trn
A wani labari na daban, hamshakin mai arzikin Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya samu N2.49 tiriliyan a cikin sa'a 24.
Asali: Legit.ng