Kotu ta ki Amincewa Da Bukatar Dakatar Da Tsarin CBN, Na Cire Kudi

Kotu ta ki Amincewa Da Bukatar Dakatar Da Tsarin CBN, Na Cire Kudi

  • 'Yan majalissar dokokin Nigeria sun bukaci babban bankin kasa da ya duba tsarin da ya fito dashi, tare da kara yawan adadin kudin da za'a iya cirewa.
  • A yau ne sabin kudin da babban bankin kasa ya buga zasu fito su fara yawo a hannun 'yan kasa.
  • Har yanzu tana kasa tana dabo kan batun sauya fasalin kudin Nigeria da kuma tsarin da babban bankin kasa ya fito da shi kan batun kayyade cire kudi

Abuja: Wata babbar kotun Abuja da ke zamanta a Maitama ta ki amincewa da bukatar dakatar da tsarin cire kudi da babban bankin Najeriya ya shigo dashi.

Masu neman sauya tsarin su 10, sune ne suka gabatar da bukatar a gaban kotun a madadin ‘yan Najeriya miliyan 20 da ba su da banki, mutanen suna karar shugaban kasa da gwamnann babban banki. Rahotan Vanguard

Kara karanta wannan

Hotuna: Yadda jirgin kasa Abuja-Kaduna ya murkushe wata mota da ta hau kan titinsa

Masu shigar da karar sun roki kotun da ta bayar da umarnin ci gaba da gudanar da mu'amala da kudin da yake hannun mutane sannan a cire ranar da kudin zai daina aiki.

Kotun
Kotu ta ki Amincewa Da Bukatar Dakatar Da Tsarin CBN, Na Cire Kudi Hoto: Vanguard
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Meyasa Suka Shigar Da Karar

Mutanen sun ce hakan kan shafar sama da ’yan Najeriya miliyan 20 da ba su da banki wadanda ke da rauni ga ga kuma rashin fasahar zamani da ake amfani da ita wajen gudanar da banki.

Mutanen sun ce ya kamata a duba dokar da ta bada damar cire N500,000 wa kamfanunuwwa da kuma 100,000 wa dai-daiku.

Sun ce ya sabawa dokar safarar kudi, kuma hakan take hakkin yan Nigeria musamman ma a bangaren kasuwanci da hada-hada a tsakanin al'umma.

Bugu da kari sun bukaci kotun da ta bayar da umarnin a gaggauta sauraron karar da kuma bayar da umarnin CBN ya samar da cikakken tsari da ka’idojin da suka shafi ‘yan kasa sama da miliyan 20.

Kara karanta wannan

Bukatu 6 da Muka Gabatarwa Buhari Sa'ilin da Muka Zauna da Shi Inji Aminu Daurawa

Bayan sauraron lauyoyin masu kara, Mai shari’a Sylvanus Oriji ya ki duba bukatun nasu, sannan yace bazai bawa babban bankin ko wanne umarni ba.

Daga nan ne alkalin ya dage sauraren karar zuwa ranar 10 ga watan Janairu, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida