Da Ciwo: Dan Najeriya Ya Dawo Daga Turai Bayan Makonni 3, Ya Tarar Mai Aiki Ta Yashe Kayan Abinci

Da Ciwo: Dan Najeriya Ya Dawo Daga Turai Bayan Makonni 3, Ya Tarar Mai Aiki Ta Yashe Kayan Abinci

  • Bayan ya shafe makonni uku a Turai, matashi dan Najeriya ya koma gidansa ya tarar da aika-aika
  • Ya gano cewa kwabansa da ke kunshe da kayan abinci kamar su taliya, magi, shinkafa, kwai da wake ya zama wayam babu komai
  • An dai gano cewa mai aikinsa ce ta yashe shi a daidai lokacin da aljihunsa ya bushe kandas

Wani dan jaridan Najeriya, Joey Akan, ya baiwa mutane mamaki bayan ya bada labarin arangamar da ya faru tsakaninsa da mai masa aikin goge-goge.

Joey ya ce ya tafi kasar Turai sannan ya dawo bayan makonni uku kawai sai ya tarar da gidansa wayam babu komai. Ta tabbata mai yi masa aikin goge-goge ce ta kwashe dukkanin kayan abinci da ya bari ciki harda katan biyu na tafiya, shinkafa, wake da magi.

Kara karanta wannan

“Na Rasa Sukuni”: Dan Najeriya Ya Koka a Bidiyo, Ya ce Matar Da Ya Aura Ya Kai Turai Tana Sharholiya Da Maza

Matashi da kayan abinci
Da Ciwo: Dan Najeriya Ya Dawo Daga Turai Bayan Makonni 3, Ya Tarar Mai Aiki Ta Yashe Kayan Abinci Hoto: blackCAT, Nigerian food items in Ghana, Chi Nigerian foodstuffs
Asali: Getty Images

Dan jaridan ya bayyana cewa abun da ya dawo ya tarar ya yi masa ciwo sosai domin ya dawo daga tafiyar aljihunsa a bushe kandas. Ba tare da bata lokaci ba ya kori mai aikin saboda abun da ta aikata. Labarin da ya wallafa a Twitter na cewa:

"Na je Turai na dawo bayan makonniu uku sannan mai aikina ta yashe kayan abincina gaba daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Katan din taliya guda biyu, sun tafi, kwai sun tafi, shinkafa, wake,m gari, buta, magi, abincin gwangwani komai.
"Kuma na dawo gida babu komai gashi bani da kudi. Abun ya mun ciwo sosai. Don haka na gaggauta sallamarta nan take."

Kalli wallafarsa a kasa:

Jama'a sun yi martani

@chily_drip ya ce:

"Idan za ka yi tafiya ka dade haka, menene dalilin da zai sa ka barwa mai aikinka makullinka? Dan uwana ya yi irin haka. Ni, Allah ya yi ni mutum mai kare kayana. Ba zan bar wa kowace mai aiki makudkkina ba dan Allah."

Kara karanta wannan

Magidanci Ya Yiwa Diyarsa Gwajin DNA a Boye, Ya Gano Ba Shine Ubanta Ba, Ya Mikawa Matar Sakamako a Bidiyo

@AllStackDev ta ce:

"Na fada ma wata mai aikin goge gida, zan dawo washegari...hajiya ta goge gidan washegaru ta kwana a ciki sannan ta gama da duk kyaututtukan da na samu daga wajen aikina, cewa diyarta na kuka ne sai ta bata don ta daina kuka duk wani abu na ci ya yi batan dabo."

@SegunOladejo_ ya ce:

"Yan Najeriya sun cika iko da abun wani. Sai ka ji mutane na fada maka ai abinci ne kawai kuma da ka kyale ta. Daga haka yake farawa. Ba mu san iyaka ba saboda muna kallon mutane a matsayin wanda ya fi mu kudi."

Yan Najeriya aun tallafawa wata tsohuwa mara gata

A wani labari na daban, mun ji cewa Allah ya tarbawa garin wata dattijuwa da ke yawo a titi nono bayan yan Najeriya sun bata tallafi.

Matar dai na yawo ne a titi kasancewarta mara galihu, sai dai Allah ya kawo mata daukaka bayan bidiyonta ya yadu a soshiyal midiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng