Tsohon Dan Majalisar Tarayya Daga Jihar Oyo, Nicholas Ojo Alokomaro, Ya Rasu
- Wani tsohon dan majalisar wakilai kuma babban basarake, Nicholas Ojo Alokomaro, ya kwanta dama
- Alakata na Akata da ke Igbomoso ya rasu a ranar Juma'a, 9 ga watan Disamba, bayan ya yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya
- Marigayin ya yi aiki a matsayin da majalisar wakilai ta tarayya daga 1992 zuwa 1993 kuma ya wakilci mazabar Ogbomoso ta kudu
Jihar Oyo - Allah ya yiwa Cif Nicholas Ojo Alokomaro, tsohon dan majalisar wakilai rasuwa.
Iyalan Ojo Alakomaro da ke Ogbomoso, jihar Oyo ne suka sanar da labarin mutuwar tasa a ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba, jaridar The Guardian ta rahoto.
Ya yi jinya kafin rasuwarsa
Legit.ng ta tattaro cewa marigayin wanda shine Alakata na Akata da ke Ogbomosoland ya rasu ne a ranar Juma'a, 9 ga watan Disamba bayan ya yi fama da rashin lafiya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Alokomaro, wanda ya kasance dan majalisar wakilai daga 1992 zuwa 1993, ya wakilci mazabar Ogbomoso ta kudu kuma ya yi aiki a matsayin mamba na kwamitin kula da Ogbomoso ta kudu.
Rahoton ya kuma kawo cewa mariyain ya mutu ya bar 'ya'ya da jikoki.
Jakadan Najeriya a kasar Spain ya rasu
A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa jakadan Najeriya a kasar Spain, Demola Seriki ya amsa kira mahaliccinsa yana da shekaru 63 a duniya a ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba.
Kamar yadda iyalan marigayin suka sanar, Seriki ya mutu ne a cikin 'ya'yansa a birnin Madrid da ke kasar Spain.
Kafin rasuwarsa, Seriki ya rike mukaman gwamnati da dama da suka hada da na karamin ministan noma da albarkatun ruwa, karamin ministan harkokin cikin gida, karamin mijistan tsaro da sauransu.
Yana kuma rike da sarautar Otun Aare na jihar Lagas.
A wani labarin kuma mun ji a baya cewa Allah ya yiwa dan majalisa mai wakiltan karamar hukumar Bakori a majalisar dokokin jihar Katsina, Dr Ibrahim Aminu Kurami, rasuwa a Saudiya.
Kamar yadda rahotanni suka kawo daga dangin mamacin, dan majalisar ya rasu ne a birnin Madina bayan ya yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya a kasar mai tsarki inda ya je yin aikin Umra.
Asali: Legit.ng