Jim Kadan Bayan Dawowarsa Bakin Aiki, Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Ya Murkushe Wata Mota

Jim Kadan Bayan Dawowarsa Bakin Aiki, Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Ya Murkushe Wata Mota

  • Hotuna sun nuna yadda jirgin kasan Abuja-Kaduna ya murkushe wata mota yayin da take kokarin ketara titinsa a Abuja
  • Ya zuwa yanzu dai ba a san ko an yi rashin rai ba, amma an ga alamar jami'an tsaro da na hukumar ba da agaji a wurin
  • Wannan na zuwa ne kasa da mako biyu da dawowar jirgin kasan bakin aiki bayan da aka dakatar dashi tun harin da 'yan bindiga suka kai kansa watanni tara baya

Kubwa, Abuja - Wasu hotunan da jaridar Aminiya ta yada sun nuna lokacin da mutane ke kan aikin ceto da ganewa idanunsu yadda jirgin kasan Abuja-Kaduna ya murkushe wata mota da ke kokarin tsallaka hanyarsa.

Wannan lamari ya faru ne a tashar jirgin da ke Kubwa a babban birnin tarayya Abuja, a daidai lokacin da yake dab fita daga cikin tashar.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Bidiyon yadda aka kirkiri injin kyankyasar jariran dan Adam

Hotunan sun nuna motar mai daunin baki, mutane sun zagaye ta domin duba halin da ake ciki, duk da cewa ba a bayyana ko direbanta ta rasu ba.

Yadda jirgin kasan Abuja-Kaduna ya murkushe mota a kan titinsa
Jim Kadan Bayan Dawowarsa Bakin Aiki, Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Ya Murkushe Wata Mota | Hoto: @aminiyatrust
Asali: Twitter

Hakazalika, alamu daga hotunan sun nuna jami'an tsaro da na hukumar agaji sun taru domin shawo kan lamarin da ake tunanin watakila ya zo da rasa ko rauni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli hotunan:

'Yan bindiga sun farmaki jirgin kasan Abuja-Kaduna

Idan baku baku manta ba, watanni tara da suka gabata ne wasu tsagerun 'yan bindiga suka kai farmaki kan jirgin kasan na Abuja-Kaduna, lamarin da ya kai ga asarar rayuka, an kuma sace mutane da dama.

Bayan dogon kai ruwa rana, an yi nasarar kubutar da mutanen da aka sacen ta hanyar biyan kudaden fansa da kuma tattaunawar da ta shiga tsakani da jami'an gwamnati.

An dakatar da jirgin daga jigilar ayyukan da yake saboda dalilai na tsaro, hakan ya ba gwamnati damar yanke shawarwari kan mataki na gaba.

Kara karanta wannan

Bukatu 6 da Muka Gabatarwa Buhari Sa'ilin da Muka Zauna da Shi Inji Aminu Daurawa

Jirgin ya dawo aiki a watan Disamba

A cikin wannan watan ne gwamnatin Najeriya ya sanar da cewa, jirgin zai ci gaba da aikin da ya saba daga babban birnin tarayya Abuja zuwa jihar Kaduna a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Wannan sanarwa ta fito ne daga hukumar zirganiyar jiragen kasa ta Najeriya, tare da bayyana sabbin ka'idoji da fasinjoji za su cika kafin shiga jirgin.

Hakazalika, an tanadi jami'an tsaro da za su ke jigilar rakiya ga jirgin domin kaucewa wani harin 'yan ta'addan a nan gaba, kamar yadda rahoto ya bayyana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.