"Na Yi Kewarki" Wani Mutumi Ya Daga Matarsa Da Ta Kai Masa Ziyarar Bazata

"Na Yi Kewarki" Wani Mutumi Ya Daga Matarsa Da Ta Kai Masa Ziyarar Bazata

  • Wata kyakkywar mata ta wallafa bidiyon yadda abokin rayuwarta ya ji bayan ta kai masa ziyarar bazata har gida
  • Matashiyar matar wacce ke zaune nesa da mijinta ta yi wani tunani, haka nan ta kai ziyarar ba zata ga rabin rayuwarta
  • A bidiyon mai ban sha'awa, Magidanci na kyalla ido ya ganta ya garzaya ya ɗaga ta sama cikin farin ciki da murmushi a fuskarsa

Wani ƙayataccen bidiyo da aka wallafa a shafin TikTik ya nuna yadda tsuntsun soyayya ya haɗa wasu ma'aurata biyu bayan shafe dogon lokaci nesa da juna.

Yayin da ta wallafa bidiyon, matar mai suna @mrs.amissah ta bayyana cewa alaƙarsu ta yi nisa kuma basu tare da abokin rayuwarta.

Soyayyar Ma'aurata.
"Na Yi Kewarki" Wani Mutumi Ya Daga Matarsa Da Ta Kai Masa Ziyarar Bazata Hoto: @mrs.amissah
Asali: UGC

A halin yanzu, ta yanke kai masa ziyarar bazata zuwa wurin da yake zaune, kuma yadda ya yi martani lokacin da idonsa ya ganta ya kwantar mata da hankali.

Kara karanta wannan

Yadda Yan Najeriya Suka Share Hawayen Wata Dattijuwa Da Ke Kwana a Titi, An Sama Mata Muhalli

A ɗan gajeren kyakkyawan bidiyon, masoyan biyu sun rungume juna kamar ba zasu rabu ba yayin da Mijin wanda ya cika da farin ciki ya ɗaga matarsa cak saboda tsabar murna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli bidiyon haɗuwar ma'auratan anan

Martanin mutane a Soshiyal midiya

@Dukezhyford ya ce:

"Idan kana tunanin aure babu daɗi, aa tsaya nan a matsayin gwauro karkayi aure."

@quameboakye1 ya ce:

"Ni kaina haka zan yi da ace ko budurwa ina da ita, na ƙagara na ga na zama Angon wata."

@tinaabynahboatemaa ta ce:

"Ikon Allah wai meyasa nake ta washe baki ina murmushi ne? Na yi takaici, rayuwar gwauranci ba daɗi."

@francababynaa ta ce:

"Wannan abu gunin kyau, tun ɗazu nake kallo na kara kallo tsawon mintuna 30."

A wani labarin kuma

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262