Kwankwaso Ya Bayyana Farin Cikinsa Yayinda AA Rano Ya Baiwa Matukan Jirgin Kwankwasiyya 6 Aiki

Kwankwaso Ya Bayyana Farin Cikinsa Yayinda AA Rano Ya Baiwa Matukan Jirgin Kwankwasiyya 6 Aiki

  • Dan takarar kujerar shugaban kasan NNPP ya yi tsokaci kan baiwa wasu matasan Kwankwasiyya aiki a kamfanin Rano Air
  • Hotuna sun nuna wasu matasa shida da gwamnatin Kwankwaso ta dau nauyin karatunsu a baya
  • Sanata Kwankwaso ya ce wannan itace babbar manufarsu ta karfafa matasa don su zama masu zaman kansu

Sabon kamfanin jirgin saman Attajirin dan jihar Kano, AA Rano, ya baiwa wasu matasan da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya dau nauyin karatunsu lokacin yana mulki.

Baba, wanda aka fi sani da Kwankwason Tuwita ya bayyana hakan a jawabi da ya fitar tare da hotunan matukan jirgin lokacin da suke karbar takardun fara aikinsu.

Yace:

"Rano Air Nigeria Limited ya baiwa matukan jirgin Kwankwasiyya 7 aiki."
Sune:
Capt. Abubakar BelloDanfulani

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa za mu zabi Tinubu a matsayin shugaban kasa – Kiristocin Kudu

Capt. Bashir Danladi Garba
Capt. Habibu Yakubu Bechi
Capt. Yunus Abba Yunus
Capt. Abdulmajid Said
Capt. Idiris Baba Idi
Capt. Umar gwarzo.
Martanin Kwankwaso

Kwankwasiya
Kwankwaso Ya Bayyana Farin Cikinsa Yayinda AA Rano Ya Baiwa Matukan Jirgin Kwankwasiyya 6 Aiki Hoto: @baba
Asali: Twitter

Tsokacin Kwankwaso

Dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana farin cikinsa bisa wannan labari.

Ya bayyana cewa wannan da ma itace manufarsa na karfafa mutane da horar da su don kamfanoni su basu aiki.

Yace:

"Jarin da muka zuba a karfafa daidaikun mutane an yi don horar da su don su samu aiki wajen kamfanoni irinsu Rano Air."
"Ina taya matasan murna da Rano Air. Na ji Dadi Sosai."

Gwamnatin taraya ta baiwa kamfanin Rano Air lasisin fara jigilar fasinjoji daga jihohin Najeriya daban-daban.

Mammalakin kamfanin ya shahara da sana'ar gidajen man fetur kuma ana yabonsa da gaskiya da amana.

Wanene Mammalakin Rano Air

Shugaban Kamfanonin AA Rano, Alhaji Auwalu Abdullahi Rano, dan asalin Kano ne.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Yi Kus-Kus da Wani ‘Dan Takaran 2023, Ya bar Magoya-baya a Duhu

Ya shiga jerin yan jihar Kano da suka shiga harkar sufurin jiragen sama a tarihin Najeriya.

Wadanda suka gabacesa sun hada da Azman, Kabo, dss.

A tashin farko, AA Rano ya sayi jiragen EMB-145LRs guda 4 don fara amfanu da su wajen jigilar fasinjoji.

Farashin jiragen

Binciken da muka gudanar ya nuna cewa farashin jiragen Embraer ERJ-145LR ba zai rasa kaiwa dalar Amurka $2,395,000 ba.

Wannan bisa rahoton GlobalAir.com.

Kamfanin Rano ya samu lasisin sufurin jiragen sama (ATL) daga wajen Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA).

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida